Cin amana kiri-kiri: Kotu ta tsare Adama wacce tayi yunkurin kwacewa babbar aminiyarta miji a jihar Kaduna

Cin amana kiri-kiri: Kotu ta tsare Adama wacce tayi yunkurin kwacewa babbar aminiyarta miji a jihar Kaduna

- Kotun Magajin Gari dake jihar Kaduna ta bada umarnin tsare wata mata mai suna Adama Arabi

- Kotun ta bada umarnin ne bayan kamata da laifin shiga gonar da ba tata ba, inda tayi kokarin kwacewa aminiyarta miji

- Alkalin kotun ya ce ba zai sake ta ba sai ta kawo mutumin da zai iya tabbatar da cewa za ta zauna har lokacin da za a kammala shari'a sannan kuma ya bayar da naira 100,000

Kotun Magajin Gari ta jihar Kaduna, ta bayar da umarnin tsare wata mata da ta yi yunkurin neman mijin babbar aminiyarta.

Alkalin kotun Mai Shari'a Murtala Nasir ya bayyana cewa yana so a tsare matar mai suna Adama Arabi, har sai lokacin da ta samu mutumin da zai biya naira 100,000 a matsayin kudin beli.

Adama wacce ita ma matar aure ce, an kama ta da laifin neman mijin babbar aminiyar tata.

Alkalin ya bayyana cewa dole sai ta samo wani mutumin da kotu za ta gamsu da shi cewar ba za ta gudu ba idan aka bukaci ganinta a kotu ranar 25 ga watan Yuli.

Bayan haka kuma alkalin kotun ya yiwa matan biyu gargadi sosai akan cewa kada su sake wata mu'amala ta sake shiga tsakaninsu domin gujewa wani sabon rikicin a tsakaninsu.

KU KARANTA: Babbar magana: Ya yiwa kakar matarshi dukan kawo wuka saboda ta kasa rarrashin jaririyarshi ta daina kuka

Fatima Sulaiman ita ce ta kai karar Adama Arabi kotun, ta hannun lauyanta Mushabu Mustapha, wanda ya bayyanawa kotu cewa da mai kawo karar da wacce ake karar manyan aminan juna ne.

Fatima wacce take harkar kasuwanci, ta na yawan bai wa Adama labarin matsalar dake tsakaninta da mijinta.

"Hakan yasa Adama tayi amfani da wannan damar ta dinga yawan zuwa gidan Fatima a duk lokacin da mijinta yake nan da shiga wacce take bayyana surar jikinta.

"Fatima dai tana da shagonta a unguwar Malali, haka Adama take daukar kafa ta tafi shagon nan ba tare da Fatima ta nemeta ba, kawai dai saboda ta san cewa mijin Fatima yana zama a shagon," in ji Lauyan.

"Bayan Adama ta gama shige da fice domin ta juyo da zuciyar mijin Fatima mai suna Sulaiman Jere, sai ta koma watsa jita-jita cewa mijin Fatima yana zuwa yana bata hakuri, kuma yana cewa yana sonta.

"Muna neman kotu ta yankewa Adama hukunci daidai da laifinta, saboda ta yiwa Fatima barazana, sannan ta butulcewa amincin dake tsakaninsu." In ji lauyan Fatima.

Sai dai kuma ita Fatima wacce ba ta da lauya ta karyata duka wadannan zargee-zarge da aka yi mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel