Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa mahaifin Makarfi rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa mahaifin Makarfi rasuwa

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un: Allah ya yiwa mahaifin tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Alhaji Ahmed Mohammed Makarfi, rasuwa.

An sanar da rasuwarsa ne da ranan nan bayan Sallar Azahar.

Sanarwar yace: "Mahaifin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ya rasu. Za;a gudanar da jana'izarsa misalin karfe 4 na yamma bisa ga koyarwan addinin Musulunci. Allah ya jikanshi da rahama."

Gwamna Ahmad Makarfi ya mulki jihar Kaduna tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, sannan ya zama Sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa tsakanin 2007 da 2011 sannan ya zama shugaban jam'iyyar PDP.

A bangare guda, rahoto ya tabbatar da mutuwar mutane 8 da hatsarin rushewar gidan sama mai hawa 2 ta rutsa dasu a garin Jos, tare da tabbatar da mutane 4 da suka samu rauni daban daban.

Hatsarin ya auku ne a ranar Litinin, 15 ga watan Yuli a Layin Butcher, unguwar Dilimi, cikin karamar hukumar jos ta Arewa, kamar yadda jaridar Legit.ng ta tabbatar inda ta ruwaito gidan mallakin Alhaji Rufai Kabiru ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel