Yadda baki 7 suka mutu a hanyarsu ta dawowa daga daurin aure a Katsina

Yadda baki 7 suka mutu a hanyarsu ta dawowa daga daurin aure a Katsina

- Wasu mutane bakwai sun mutu nan take bayan hatsarin mota ya ritsa da su a hanyarsu da dawowa daga wurin daurin aure

- An gano cewa mutanen da suka yi hatsarin na kan hanyarsu ta dawowa Zaria ne bayan sun halarci wani daurin aure a Funtuwa

- Kimanin wasu mutane takwas sun samu raunuka sakamakon hatsarin da ya afku tsakanin wata Kanta da Sharon

Wasu mutane bakwai sun mutu yayin da wasu takwas suka samu munanan raunuka sakamakon hatsarin mota da ya ritsa da su ranar Lahadi a kan hanyar Funtuwa zuwa Zaria.

Hatsarin mota ya ritsa da mutanen a dadai kauyen Bakin Dutse.

An gano cewa mutanen da suka yi hatsarin na kan hanyarsu ta dawowa Zaria bayan sun halarci wani daurin aure a Funtuwa.

DUBA WANNAN: Kotu ta daure malamar makaranta bayan samunta da laifin yin lalata da dalibi mai shekaru 13

Abdullahi Danladi Ibrahim, kakakin hukumar kiyaye hadura na ofishin shiyyar yankin da hatsarin ya faru, ya tabbatar da afkuwar lamarin. Ya ce hatsarin ya faru ne a tsakanin wasu motoci biyu; kanta kirar Toyota mai lambar XA 480 KEF da wata Volkswagen Sharon mai lambar AZ 171 KMC.

"Sun yi taho mu gama ne kuma nan take mutane bakwai suka mutu, yayin da aka garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti domin basu kulawa," a cewar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel