Tirkashi: Amaechi ya fede biri har wutsiya, ya bayyana 'yan siyasar da suka sace kudi suka azurta kansu a kasar nan

Tirkashi: Amaechi ya fede biri har wutsiya, ya bayyana 'yan siyasar da suka sace kudi suka azurta kansu a kasar nan

- Amaechi ya bayyana cewa ya san da yawa daga cikin 'yan siyasar kasar nan da suka saci kudade suka azurta kansu

- Ya ce wadannan kudade da suka sata kamata yayiace anyi amfani da su wajen gina hanyoyi da abubuwan more rayuwa na al'umma

- Sannan ya bayyana cewa 'yan Najeriya ba su damu da satar da 'yan siyasa ke yi ba shine yasa ko damuwa ba sa yi akan a hukunta su

Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa Najeriya kasa ce da ba a damu da bin doka ba, inda ya kara da cewa 'yan Najeriya basa ganin laifin 'yan siyasa akan matsalar talaucin da suke ciki.

Amaechi ya bayyana cewa ya san 'yan siyasar da kafin su samu mulki basu da ko anini, amma suna hawa mulki suka mayar da kansu hamshakan masu kudi.

Da yake magana a wajen wani taro da aka yi akan matasan 'yan siyasa masu tasowa a jihar Legas, Amaechi ya ce akwai bukatar 'yan siyasa su bayyana yadda suke so fitar da mutane daga cikin kangin talaucin da suke ciki.

KU KARANTA: Wani abu sai Najeriya: Kwantena biyu da gwamnatin tarayya ta sayo na kayan gyaran wutar lantarkin sun yi batan dabo a tashar jiragen ruwa

Ya ce: "Na san 'yan siyasar da suka saci makudan kudade suka azurta kansu, kuma wannan kudade da suka sata kamata yayi ayi amfani da su wajen gina hanyoyi da sauran ayyukan more rayuwa ga al'umma.

"Ya kamata 'yan siyasar mu su fito karara su bayyanawa al'umma hanyoyin da zasu bi su fitar dasu daga cikin wannan kangin talaucin da suke ciki."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng