Allah ya kyauta: Dalibi dan shekara 14 ya bayyana dalilin da ya sanya ya shiga kungiyar asiri

Allah ya kyauta: Dalibi dan shekara 14 ya bayyana dalilin da ya sanya ya shiga kungiyar asiri

-Wani dalibi mai shekaru 14 dan makarantar karamar sakandare ya bayyana cewa ya shiga kungiyar yan daba ne don ya kare kanshi daga zalunci

-Matashin mai suna Christopher Anthony ya bayyana hakan ne a lokacin da yan sanda suka kamashi

-Daga bisani komishinan yan sanda na jihar yayi kira ga iyaye da su mike tsaye wajen tarbiyyantar da 'ya'yansu

Wani dalibi mai shekaru 14 dan makarantar karamar sakandare mai suna Chrisptopher Anthony ya bayyana cewa ya shiga kungiyar yan daba ne don ya yaki wasu makiyanshi ya kuma kare kanshi daga zalunci.

Yaron ya bayyana cewa shi mazauni ne a Kauyen mutum daya (One-Man) dake a karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa, ya kuma amsa laifin da ake zarginsa da shi bayan da yan sanda suka kama shi a garin Lafiya.

Komishinan yan sanda na jihar Nasarawa, Bola Longe ya yi kira ga iyaye da su mike su sauke nauyin da Allah ya dora masu na tarbiyar 'ya'yansu.

Ya ce “Ina kira ga iyaye da su sauke nauyin da ke kansu a matsayinsu na iyaye ta hanyar horar da yaransu su zama nagari kuma su rinka lura da halayyar ‘ya’yansu musamman wadanda suke a makarantar sakandare da jami’o’i”

KARANTA WANNAN: Gobara ta lashe kasuwar kantin Amigo da ke Abuja

Komishinan yayi gargadi ga yan ta’adda da sauran masu laifi cewa rundunar yan sanda ba za ta gajiya ba wajen ganin ta magance duk wani matsalar ta’addanci a jihar.

Jaridar Dailytrust ta ruwaito cewa kwanan nan rundunar yan sandan ta jihar Nasarawa ta kama wasu yan ta’adda su 32 wanda mafi yawansu yan makarantar sakandare ne a karamar hukumar Karu dake a jihar Nasarawa.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel