An kama wata mata na zina da wanda ya kashe mijinta

An kama wata mata na zina da wanda ya kashe mijinta

-Wata mata ma'aikaciyar asibiti ta shiga hannun 'yan sanda bayan an same ta da laifin biyan wasu katti biyu kudi domin su kashe mijinta

-Matar mai suna Ajemine Douglas ta kasance ta na kwanciya da Kingsley Nna bayan ya kashe mijinta tare da abokinsa Sunny

Wata mata wadda ke aiki da Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Rivers, Douglas Ajemine ta shiga hannun ‘yan sanda bayan da aka same ta da laifin biyan wasu katti biyu domin su kashe mijinta.

Matar mai shekaru 41 da haihuwa, an kamata ne a unguwar Abalama wadda kuma ta kasance tana aikata zina da Kingsley Nna bayan ya kashe maigidanta mai suna Inedugoba Tyger.

KU KARANTA:Zaben Zamfara: Kotun korafin zabe ta dage sauraron karar zaben Gwamna

Ajemine ta bada labarin aukuwar wannan lamarin kamar haka: “ A watan Disemban shekarar 2014 na hadu da Inedugoba Tyger kuma mu kayi aure bayan shekara guda. Ko kafin ya aure ni ya na da yara biyu kuma ya roke ni cewa in taimaka mashi in kula da yaran.

“ Na amince da wannan kudurin nasa, muka zauna a gidansa tare da wadannan yara. Muna zaman lafiya da shi har zuwa lokacin da aka kore shi daga aiki. A daidai wannan lokacin ne muka fara samun sabani da shi, har ta kai wani lokaci yazo yana neman sayar da kayayyakin gida ni kuma sai in hana shi.

“ Da na gaji da zama da shi, na yi hijira na bar masa gidansa dake Abalama na koma Fatakwal. A hankali ya nemo sabon mazaunin nawa kuma ya fara zuwa a kai a kai. Duk sanda yazo sai ya nemi yin jima’i da ni kuma ta karfi.

“ Abinda mijin nawa ke yi ya fara damuna sai na nemi Kingsley Nna ta waya cewar ya kawo min dauki ga abinda mijina keyi mani.”

Bayan Kingsley da abokinsa Sunny sun kashe mijin matar, sai alaka sabuwa ta kullu tsakanin Ajemine da Kingsley inda suka kasance tamkar mata da miji, a otal suke haduwa domin sheke ayarsu, kamar yadda Kingsley ya fadi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel