Tirkashi: Wasu mata sun sace jaririya daga zuwa barka a Zariya

Tirkashi: Wasu mata sun sace jaririya daga zuwa barka a Zariya

- Wasu mata guda biyu sun sace jaririya a garin Zariya daga zuwa yiwa mahaifiyarta barka

- Matan sunje sanye da nikabi a fuskarsu, inda suka yiwa mai jegon dabara suka gudu da jaririyar

Wani abu da ya faru a garin Zariya mai ban mamaki, yayin da 'yan barka suka sace wa wata mata jaririyar ta daga zuwan su barka a unguwar Layin Malam Mai Bulala dake yankin Samaru cikin karamar hukumar Sabon Gari Zariya dake jihar Kaduna.

Wakilin jaridar Leadership ya ziyarci gidan da lamarin ya faru kuma ya zanta da mahaifiyar jaririyar.

Malama Nafisa ita ce mahaifiyar jaririyar wacce 'yan barka suka sace ana gab da sallar Magariba a gidansu inda take zaune ita da mai gidanta Kyauta Mai Dusa.

Nafisa ta bayyana cewa: "Wasu mata guda biyu ne suka shiga gidan kowacce ta rufe fuskarta da nikabi, suka je da niyyar yi mata barka. Bayan sun gama gaisawa, sai suke tambayata ina mijina? Na ce musu ya fita, sai suke ce mini su matan abokinsa ne, sun zo tare da mijinsu yana waje yana jiransu domin ganin jaririya."

Wannan magana ce ta sa Nafisa ta yadda da wadannan mata har ta dauki jaririyar ta basu domin su gani.

Me zai faru? Malama Nafisa na mika musu jaririya, sai suka ce mata, "to bari mu kai wa mijinmu jaririyar ya ganta a kofar gida." Ita kuma mai jego ba ta kawo komai a ranta ba sai ta ce musu to ba damuwa,.

KU KARANTA: Kano: Ta kashe kanta saboda mutuwar auren iyayenta

Bayan matan sun fito da jaririyar da kusan mintuna 30 sai mai jego ta ji shiru. Sai ta leko kofar gida, ba ta ga kowa ba. Cikin gaggawa ta koma gida ta sanar da mutanen gidan halin da ake ciki.

Bayan ta sanar da mutanen gidan sai suka sanar da mahaifin yaron, wanda yake a masallaci yana sallar Magariba a lokacin. Nan take suka fito suka bazama cikin unguwar suna cigiyar mata guda biyu sanye da nikabi.

Sai da aka kwashe kwanaki biyu cur ana neman matan, a kwana na uku ne aka ji labarin wata mata ta jefar da jariri a unguwar Gaiba kusa da gidan mai unguwar wanda ake kira Malam Hamisu.

Hakan ya sa mutanen da abin ya shafa suka garzaya unguwar tare da mai jegon da aka yiwa satar.

Cikin ikon Allah sai aka ga jaririyar da aka sace ce, cikin gaggawa mahaifiyar ta dauketa ta bata mama ta sha.

Rahotanni ya nuna cewa, 'yan unguwar dai tun daga lokacin suka hana zuwa barkar haihuwa cikin dare.

Mahaifin jaririyar Malam Yarima yayi godiya ga 'yan uwa da abokan arziki da suka taimaka da addu'o'i, ya kuma yi musu addu'ar Allah ya saka musu da alkhairi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel