Kano: Ta kashe kanta saboda mutuwar auren iyayenta

Kano: Ta kashe kanta saboda mutuwar auren iyayenta

- Wata budurwa ta kashe kanta saboda iyayenta sun samu sabani wanda har ya kai su ga rabuwa

- Yarinyarta sha madarar fiya-fiya ne, wadda mahaifiyarta ta ajiye domin kashe kwari

- Rahotanni sun nuna cewa kwana kadan ya rage saurayin yarinyar ya turo iyayensa domin ayi maganar aure

Wata budurwa mai suna Sadiya Shehu, 'yar shekaru 17 a duniya wacce ke zaune a unguwar Tudun Murtala dake karamar hukumar Nasarawa cikin jihar Kano, ta kashe kanta saboda wani sabani da ya shiga tsakanin mahaifanta, wanda har yayi sanadiyyar rabuwarsu.

Sadiya ta rasu bayan ta sha madarar fiya-fiya, wanda yake ajiye a dakin mahaifiyarta saboda kashe sauro da kwari.

A yayin da jaridar Aminiya ta kai ziyara gidan da lamarin ya faru a unguwar ta Tudun Murtala, Aminiya ta tarar da dumbin mutane suna tururuwar zuwa gidan don yin jaje ga iyayen yarinyar.

KU KARANTA: Sheikh Gumi: Duk wanda ya sanya hannu akan dokar wa'azi yayi ridda

Malam Shehu Lawan shi ne mahaifin marigayiya Sadiya, ya bayyana cewa Sadiya ta kashe kanta ne saboda 'yar karamar malsata da ta shiga tsakaninsa da mahaifiyarta, inda kuma daga baya suka gano bakin zaren a tsakaninsu.

"Na samu matsala da mahaifiyarta, inda hakan ya batawa Sadiya rai, saboda ta yi ta faman kuka akan wannan matsala dake tsakani na da mahaifiyarta, daga baya naje na rarrasheta akan cewa komai ya wuce munyi sulhu.

"Safiya nayi na fita wurin aiki na bar Sadiya tare da 'yan uwanta a gida. Ina wurin aiki sai aka kirani a waya ake fada mini cewa an wuce da ita asibiti. Likitoci sun yi iya bakin kokarinsu, amma da yake Allah ya kaddara cewa babu sauran kwana ta rigamugidan gaskiya."

Da jaridar Aminiya ta tambayi Malam Shehu ko an tsayarwa da Sadiya miji, sai ya ce tana da wanda yake nemanta, domin kuwa har yazo sunyi magana kuma yayi alkawarin cewa zai turo magabatansa da zarar mahaifinsa ya dawo daga kasar Saudiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel