Da duminsa: Masu dukiya sayen shari’a sukeyi a Najeriya -Lawan

Da duminsa: Masu dukiya sayen shari’a sukeyi a Najeriya -Lawan

-Sanata Lawan Ahmad yace masu kudi a Najeriya sunfi karfin shari'a.

-Shugaban masu rinjaye na majalisar yayi wannan furucin ne ranar Laraba a majalisa yayin da suke kokarin tabbatar da Abubakar Musa Sadik a matsayin shugaban Customary Court of Appeal ta Abuja.

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Najeriya, sanata Lawan Ahmad a ranar Laraba yace Najeriya kasa ce wacce idan kana da kudi kafi karfi karfin doka domin sai hukunci da kaso za’a yanke ma.

A cewarsa yadda rassan gwamnati gudu uku ke aiki a kasar nan a bayyane yake. Shugaban masu rinjayen yayi wannan maganar ne ranar Laraba yayin da majalisarsu ke zamanta na mako da ta saba inda majalisar ke kokarin tabbatar da Abubakar Musa Sadik a matsayin shugaban kotun data shafi kananan laifuka wato Customary Court of Appeal, Abuja.

Da duminsa: Masu dukiya sayen shari’a sukeyi a Najeriya -Lawan
Da duminsa: Masu dukiya sayen shari’a sukeyi a Najeriya -Lawan
Asali: Depositphotos

KU KARANTA:Shin ko me ya hana tsoffin shugabannin Najeriya zuwa wajen rantsar da Buhari?

Lawan yace, “ Wannan shi ne hakikanin gaskiyar yadda rassa gwamnatinmu ke aiki. Mun dakatar da komi cak domin wannan tabbatarwa a yau.

“ Al’ummarmu wata irin al’umma ce wacce da zarar mutum na da tarin dukiya sai aikata abinda ya ga dama. Muna fatan a yanzu zamu canji a wannan bangaren.” Inji Lawan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel