Yadda muggan karnuka sun kaiwa jami'an EFCC hari yayin wata sumame a Ibadan

Yadda muggan karnuka sun kaiwa jami'an EFCC hari yayin wata sumame a Ibadan

Wasu muggan karnuka sun kaiwa jami'an Hukumar Yaki da rashawa EFCC hari a unguwar Agara da ke Ibadan a ranar Laraba yayin da suka kai sumame gidan wasu da ake zargin 'yan damfara ta yanar gizo.

Jami'an na EFCC sun kai sumamen ne bayan samun bayanan sirri hakan yasa suka tafi domin gudanar da bincike a safiyar ranar amma a maimakon a bude musu kofa su shigo su gudanar da bincikensu bayan sun gabatar da kansu, daga daga cikin wanda ake zargin ya umurci mai gadinsa ya sakar musu karnuka.

Sai dai wannan dabarar ba tayi aiki ba domin jarruman jami'an na EFCC sun ci galaba a kan karen sannan suka gudanar da bincike a gidan tare da kama wadanda ake zargin.

Yadda muggan karnuka sun kaiwa jami'an EFCC hari

Yadda muggan karnuka sun kaiwa jami'an EFCC hari
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Rikicin masarautar Kano: Bashir Tofa, Usman Bugaje da wasu manya sun saka baki

Kazalika, daya daga cikin wadanda ake zargin ya buga wayarsa da kasa domin hana jami'an bincika cikin wayar ko za su samo bayannan da za su taimakawa bincikensu.

Sai dai duk da hakan, jami'an sun dauki fasashiyar wayan sun tafi da ita dakin gwaje-gwaje inda ake mata binciken kwa-kwaf domin gano abinda ke cikin tun da fari.

Mataimakin shugaban EFCC na yankin, Bright Igeleke wanda ya jagoranci kai sumamen ya ce irin wannan abinda ya faru dama yana daga hadduran da ake iya cin karo da shi a aikinsu.

Wadanda aka kama a gidan sun hada Paul Afolabi, Balogun Ibrahim Adebayo, Izu Ibobo Chukwunalu, Abe Tolulope, Onifade Gidion Idowu, Komolafe Tosin da Igwe Kinsley Otuu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel