Mai martaba Sarkin Bichi ya yi fatali da maganan samun baraka tsakaninsa da Sarkin Kano

Mai martaba Sarkin Bichi ya yi fatali da maganan samun baraka tsakaninsa da Sarkin Kano

Mai martaba Sarkin Bichi, kuma daga cikin sabbin manyan Sarakunan jahar Kano guda hudu da gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta kirkiro, Sarki Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa akwai bukatar jama’a su karbi wannan lamari a matsayin daga Allah ne.

Sarkin ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da majiyar Legit.ng jim kadan bayan ya amshi sandan girma daga Gwamna Ganduje a ranar Asabar, 11 ga watan Mayu, inda yace bashi da wata burin a ganin an raba masarautar Kano saboda tana kawo hadin kai.

KU KARANTA: Yadda wani ya aikata ma Fulani danyen aiki yayi awon gaba da garken shanunsu duka

Mai martaba Sarkin Bichi ya yi fatali da maganan samun baraka tsakaninsa da Sarkin Kano
Sarkin Bichi
Asali: UGC

“A rayuwata bani da wani buri naga an raba rarraba masarautar Kano, domin mun san tana kawo kan al’umma gaba daya, to amma babu abinda al’umma zasu iya yi, sai dais u karbi wannan yanayi da Allah ya kawo sakamakon wasu dalilai da gwamnati ta hanga.” Inji shi.

Idan za’a tuna a makon data gabata ne majalisar dokokin jahar Kano ta gudanar da karatu na daya, na biyu dana uku game da kudirin yi ma dokar masarautar Kano garambawul tare da bukatar samar da sabbin masarautu masu cin gashin kansu guda hudu, inda daga bisani suka mika ma gwamna ya rattafa hannu akan kudurin ta zama doka.

Wannan doka ta samar da sabbin masarautu guda hudu da manyan sarakuna masu daraja ta daya guda hudu wadanda matsayinsu ya tashi daga hakimai suka yi daidai da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero

Sauran sun hada da Sarkin Karaye Dakta Ibrahim Abubakar, Sarkin Rano, Alhaji Tafida Abubakar II da kuma Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir. Kuma duk kuwa da cewa wata babbar kotu ta dakatar da gwamnatin daga mika rantsar dasu, amma Ganduje ya rantsar dasu tare da basu sandan girma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel