Takarar neman shugabancin majalisa da nake ya samo asali ne daga abokan aikina – Lawan Ahmed

Takarar neman shugabancin majalisa da nake ya samo asali ne daga abokan aikina – Lawan Ahmed

Shugaban masu rinjaye a majalisan dattawa, Ahmed Lawan, yace ra’ayinsa na son zama shugaban majalisan dattawa ya kasance muradin abokan aikinsa, da sabbin sanatoci.

Lawan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, a lokacin da ya bayyana a taron kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Abuja.

Dan majalisan, wanda ke wakilta yankin Arewacin Yobe a majalisar dokokin kasar, yace yana da kwarewa wajen gudanar da ayyukan shugabancin majalisan.

“Abu mai muhimmanci guda daya a shugabancin majalisa shine kwarewa. Mun yi bauta a majalisar dokokin kasa har kusan shekara ashirin.

Takarar neman shugabancin majalisa da nake ya samo asali ne daga abokan aikina – Lawan Ahmed
Takarar neman shugabancin majalisa da nake ya samo asali ne daga abokan aikina – Lawan Ahmed
Asali: UGC

“Nayi aiki tare da sauran mambobi a majalisan a lokacin baya tare da yawancin sanatocin majalisar.

“Wannan yasa na samu hadin kai daga abokan aikina, na kuma samu karuwa da kwarewa a tarayya da mu'amala dasu.

“Na koyi darusa da abubuwa da yawa daga shuwagabannin majalisar dokoki wadanda nayi aiki tare dasu."

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Buhari na cikin ganawar sirri da shugabannin tsaro karo na 2 cikin sa’o’i 48

Sanata Lawan ya ba yan Najeriya tabbacin cewa shugabancin shi zai tabbatar da adalci da gaskiya da kuma kulawa.

Yace dangane da taken yakin neman zaben shi, zai so ya kasance da majalisa mai yiwa yan Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel