Jerin wasu ayyuka 9 daya kamata Musulmi ya ya dage da aikatawa a Ramadan

Jerin wasu ayyuka 9 daya kamata Musulmi ya ya dage da aikatawa a Ramadan

A daren Lahadi, 5 ga watan Mayu ne mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar da fara azumin Ramadana, inda yace sun samu labarin ganin sabon watan Ramadana a jahohin Yobe, Sokoto da Kebbi.

Legit.ng ta ruwaito a ranar Litinin, 6 ga watan Mayu, wanda yayi daidai da 1 ga watan Ramadana ne Musulman duniya suka dauki azumi dake alanta shiga watan Azumin Ramadana, watan da Allah mai girma da daukaka Ya saukar da Al-Qur’ani.

KU KARANTA: Ramadana: Abubuwa 5 da aka haramta ma duk wani Azumi

Jerin wasu ayyuka 9 daya kamata Musulmi ya ya dage da aikatawa a Ramadan

Jerin wasu ayyuka 9 daya kamata Musulmi ya ya dage da aikatawa a Ramadan
Source: UGC

Da wannan ne muka kawo muku wasu kyawawan ayyukan alheri guda 9 da ake kwadaitar da duk mai azumi ya dinga aikatawa domin samun gwaggwabar lada da kusanci ga Allah mai tsarki da daukaka.

Daga cikin wadanna ayyukan alheri da ka iya janyo ma Musulmi kabakin alheri akwai;

1- Karatun Qur’ani

2- Sadaka

3- Ziyartar marasa lafiya

4- Ambaton Allah

5- Sallar dare

6- Salla a cikin lokacinta

7- Sauraron Tafsiri

8- Samun dacewa da daren Lailatul Qadari

9- I’itikafi

A hannu guda kuma, watan Azumi nada wasu muhimman fa’idoji da suka hada da kara ma Musulmi Imani, sanya ma Musulmi tausayin na kasa, rage ma dan Adam sha’awa, kariya ne ga Musulmi daga azabar wuta, kankare zunubbai, ceton Musulmi a ranar kiyama, da kuma shiga Aljannah ta kofar Rayya.

Sauran sun hada da kara dankon 'yan uwantaka da zumunta a tsakanin Musulmai, samar da kiwon lafiya mai inganci kama daga tsafta zuwa lafiyar jiki, samar da cikakken nutsuwa ga Musulmi yayin gudanar da ibada da kuma sanya Musulami su kasance masu juriya a lokcin kunci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel