Za a kaddamar da babban Masalacin Juma’a na Lafia a yau

Za a kaddamar da babban Masalacin Juma’a na Lafia a yau

A yau Juma’a, 3 ga watan Mayu ne za a kaddamar da babban masalacin Juma’a na garin Lafia, babbar birnin jihar Nasarawa wanda aka gyara.

Gwamnan jihar, Alhaji Umaru Tanko Almakura ne ya sanar da hakan lokacin da ya karbi bakuncin babban mamba a masarautar Lafia, Madakin Lafia, Alhaji Ishaku Dauda a yayin rangajin duba matakin da aikin ya kai kafin bikin bude shi.

An gyara masallacin ne domin ya dauki masu bauta da dama sannan kuma a kawata shi da kayayyakin zamani.

Za a kaddamar da babban Masalacin Juma’a na Lafia a yau
Za a kaddamar da babban Masalacin Juma’a na Lafia a yau
Asali: UGC

Almakura yace: “Bikin gabatar da ma’aikatan ofishin mai martaba, sabon sarkin Lafia na 17 akan mulki, Justis Sidi Dauda Bage, da kuma bude babban Masallacin Juma’a na Lafia zai gudana a ranar Juma’a, 3 ga watan Mayu , 2019.”

Gwamnan da tawagarsa sun yi shawagin duba masarautar sarkin Lafia da babban masallacin Juma’a don tabbatar da gabatar da sallar Juma’a na farko a Masallacin cikin nasara.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga: Majalisar wakilai tayi na’am da cikakken aikin sojoji a jihar Katsina

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa kotun kolin kasar Saudiyya ta yi kira ga dukkanin Musulmi da su nemi jaririn water Ramadan a ranar Asabar, 4 ga watan Mayu sannan su sanar da kotu mafi kusa game da wadanda suka ga watan ido da ido ko kuma ta abun hangen nesa, kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya ta ruwaito.

Kotun kolin ce ta sanar da hakan a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu, yayinda ake sanya ran fara azumin watan Ramadana a ranar Lahadi sannan a ci gaba har zuwa farkon watan Yuni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel