Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ta dauki fasinjoji 1.5m cikin kwana 1,000

Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ta dauki fasinjoji 1.5m cikin kwana 1,000

Bayan aiki na kwana 1,000, ma’aikatar jirgin kasan Nigeria (NRC) ta yi sufuri da akalla fasinjoji 1.5m daga Abuja zuwa kaduna, ta jirgin kasa, lissafin ma’aikatar NRC ya bayyana haka.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin jirgin a ranar 26 ga watan yuli 2016, wanda shine jirgin safarar mutane na farkon da injiniyoyin kamfanin China suka gina ta hanyar biyan kashi 75 na kudi da kuma kashi 25 daga Nigeria.

Yayinda yake magana a taron murnar wannan nasara, shugaban NRC, Fidet Okhiria, yace “Babbar nasara ne ace jirgi yayi aiki na tsawon kwana 1,000 ba tare da hadari, matsala ko tsari ba, kuma bamu bar aiki kona kwana daya a ciki ba.”

Jirgin kasan hanyar Abuja zuwa Kaduna na daukar fasinjoji 1.5m a kwana 1,000
Jirgin kasan hanyar Abuja zuwa Kaduna na daukar fasinjoji 1.5m a kwana 1,000
Asali: Twitter

Bisa ga bayanin shi, yace mutane na kokawa cewar hukumar bata wanzar da aiki ishasshe, amma komai a hankali yake tafiya, sannan ya bada tabbacin cewa zasu kara yawan adadin jiragen.

“Zuwa karshen shekaran nan, Zamu samar da jirgin da zai rika zuwa yana dawowa duk awa daya. Mun biya kudin sabbin jiragen kuma za su fi wadannan kyau da dadin tafiya,”

“Maganan siyar da tikiti ta yanar gizo kuma, mun samu cigaba a kai, amma wajibi ne mubi a hankali. Mun yi talla kuma sama da kamfanoni 1,000 sun shigar da takardunsu. A yanzu haka kamfanoni uku ciki suna bayanin gaban ICPC.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel