Watsi da hadisin Annabi ya janyo ma wani makwabci shiga tsaka mai wuya

Watsi da hadisin Annabi ya janyo ma wani makwabci shiga tsaka mai wuya

Ga duk wani Musulmi mai karatu ya sani cewa Annabin Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya umarci duk Musulmi ya girmama makwabcinsa, kuma ya fadi alheri ko yayi shiru, toh amma a yanzu a iya cewa dadin duniya ya rude wasu musulman, basu girmama wannan umarni na Annabin tsira.

Irin wannan biris da koyar Annabin ce ta tsoma wasu makwabta biyu cikin tashin hankali bayan kaurewar rikici tsakanin wasu makwabtan juna a jahar Legas, Habeeb Mustapha dan shekara 19 da Yusuf Hamza.

KU KARANTA: A lura a gane: Jerin sharudda 10 da hukumar kwastam ta gindaya ma masu son shiga aikin kwastam

Legit.ng ta ruwaito Yusuf a Habeeb dukkaninsu mazauna layin Adepitan ne, cikin unguwar Alapere, a yankin Ketu na jahar Legas, amma da rikici ya kaure tsakaninsu sai Yusuf ya hau dokin zuciya ya burma ma Habeen wuka a ciki.

Dansanda mai shigar da kara, Sufeta Lucky Ihiehie ya bayyana ma kotun cewa Yusuf ya aikata hakan ne a ranar 8 ga watan Afrilu, kuma ya aikata ma Habeeb wannan danyen aiki ne sakamakon rashin jituwa daya faru a tsakaninsu, sai dai Habeeb bai kai ga mutuwa ba, amma ya lahanta shi.

A jawabin Dansandan, laifin da Yusuf ya aikata ya saba ma sashi na 245 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Legas na shekarar 2015, kuma sashin ya tanadar da hukuncin zaman Kurkuku na tsawon shekaru 15 ga wanda ya aiakata hakan.

Sai dai da kotu ta baiwa Yusuf damar magana, sai ya musanta dukkanin tuhume tuhumen da ake masa, don haka bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu sai Alkali Kubeinje ta bada belin Yusuf akan kudi N500,000, tare da mutane biyu da zasu tsaya masa akan dubu dari biyar biyar.

Daga karshe ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Mayu na shekarar 2019, kwana daya kafin rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya karo na biyu kenan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel