Yanzu-yanzu: An nada sabon shugaban kasar Algeriya

Yanzu-yanzu: An nada sabon shugaban kasar Algeriya

Majalisar dokokin kasar Aljeriya ta nada shugaban majalisar dattawan kasar, Abdelkader Bensalah, a matsayin shugaban kasa mai rikon kwarya sakamakon murabus din tsohon shugaban kasa Abdelaziz Bouteflika bayan makonni ana zanga-zanga kansa.

Majalisar dokokin ta alanta Abdelkader Bensalah, a matsayin shugaba mai rikon kwarya na tsawon kwanaki 90 kamar da kundin tsarin mulkin kasar ta tanada kafin a gudanar da sabon zabe.

Daliban kasar Aljeriya sun gudanar da zanga-zanga a birnin kasar, Algiers, na tsawon makonni domin ganin cewa lallai sai Bouteflika ya sauka daga ragamar mulki.

Mun kawo muku rahoton cewa shugaban kasar Algeria, Abdelazez Bouteflika, ya yi murabus biyo bayan tsanantar zanga-zanga da 'yan kasar ke yi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar (APS) ya rawaito.

KU KARANTA: Sai an tsige Magu kafin 29 ga watan Mayu - Wasu gwamnoni na Sanataco na shirya tuggu

Shugaban ya yanke shawarar yin murabus ne bayan daruruwan jama'a sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da sabuwar gwamnatin sa a birnin Algiers, hedikwatar mulkin kasar Algeria.

Masu zanga-zangar na dauke da takardun da ke bayyana zabin sabbin nade-naden gwamnatinsa a matsayin wanda ya saba da bukatar jama'a.

Bouteflika ya ki canja matakin nada kan sa a matsayin ministan tsaron kasar Algeria a sabuwar gwamnatin rikon kwarya da ya kafa a ranar Lahadi duk da adawa da hakan da jama'a su ka nuna.

Gwamnatin rikon kwaryar karkashin jagorancin Noureddine Bedoui ta kunshi ministoci 27, da suka hada da wasu 6 daga tsohuwar gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel