Yanzu Yanzu: Buhari yayi jawabi ga shugabannin duniya a Dubai, ya koka kan amfani da na’urar zamani wajen magudin zabe

Yanzu Yanzu: Buhari yayi jawabi ga shugabannin duniya a Dubai, ya koka kan amfani da na’urar zamani wajen magudin zabe

- Shugaban kasa Buhari yayi jawabi ga shuwagabannin akan muhimmancin kimiyar zamani

- Shugaban kasan Najeriya yace duk da cewa kimiyar zamani na canza duniya kusan kullun, akwai bukatan ayi tsare tsare don kiyaye hatsarrukan dake iya aukuwa kamar murdiyar zabe

- Buhari har ila yau yayi amfani da taron wajen yin magana akan nasarorin da matasan Najeriya suka samu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira shuwagabannin duniya da su samar da hanyoyi da za’a zamanantar da mutanen duniya da ababen qere-qere wadanda kowa zai iya mora cikin sauki da tsaro.

A cewar wani jawabi daga kakakin shugaban kasa, Femi Adesina a Abuja, shugaban kasar ya bayyana kalubalen a jawabin da yayi a taron zuba jari na shekarar 2019 a Dubai a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu.

Shugaban kasar yace akwai bukatar killace martabar Tattalin arziki mai tafiya da fasahohin zamani.

Yanzu Yanzu: Buhari yayi jawabi ga shugabannin duniya a Dubai, ya koka kan amfani da na’urar zamani wajen magudin zabe
Yanzu Yanzu: Buhari yayi jawabi ga shugabannin duniya a Dubai, ya koka kan amfani da na’urar zamani wajen magudin zabe
Asali: Facebook

Taken taron shine: “Mapping the Future of Foreign Direct Investment: Enriching World Economies through Digital Globalisation.”

Yayinda yake jawabin cewa kayan kimiyar zamani na duniya na kawo sauyi a duniyar kusan kullun, shugaban Najeriyan ya yi gargadin cewa kimiyar zamani da ya game duniya zai ci gaba da zama barazana idan aka barshi ba tare da kula ba.

Yanzu Yanzu: Buhari yayi jawabi ga shugabannin duniya a Dubai, ya koka kan amfani da na’urar zamani wajen magudin zabe
Buhari yayi jawabi ga shugabannin duniya a Dubai
Asali: Facebook

Shugaban kasar ya koka kan yadda ake amfani da kimiyar ta zamani wajen magudin zabe, karkatar da yancin damokradiyyar al’umman kasa da kuma tayar da rikici.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi na musamman a Dubai (Hotuna)

Ya kuma koka akan yawaitar labaran karya da ta’addancin da ake yi ta yanar gizo, musamman yanda yan ta’adda ke shiga shafukan mutane sannan suyi yadda suka ga dama ba tare da izini ba.

Shugaba Buhari, ya yi kira da a hada kai da fara tsakanin shugabannin gwamnati da na hukumomi masu zaman kansu domin magance barazanar da na’urar zamani ke fuskanta.

A cewarsa, kayan kimiyar zamani da ya game kan duniya ya zamo babban jigo na kyawan aiki da kuma mumuna.

Yace: “A Najeriya, amfanin wayoyin hannunmu ya zartar ma kaso tamanin. Hakan na nufin mafi akasarin yan Najeriya miliyan dari daya da casa’in na amfani da kimiyar zamani da duniyar yanar gizo."

Shugaban kasar ya kuma bayyana tarin ci gaba da aka samu a kasar Najeriya ta wannan fanni musamman a tsakanin matasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel