An fara wanzar da Shari'ar Musulunci a kasar Brunei

An fara wanzar da Shari'ar Musulunci a kasar Brunei

Kasar Brunei Darus-Salam ta fara wanzar da dokokin shari’ar Musulunci a karamar kasar dake nahiyar Asiya.

Hakan ya kunshi tsayar da haddi kan duk wanda aka samu da laifin zina ko luwadi ta hanyar jifan, yayinda za a rika yanke hannun barawo, hukuncin kisa kan 'yan fashi da makami, masu yi wa mata fyade, da kuma yin bulala ga mazinata marasa aure.

Kasar Brunei dai na karkashin mulkin Sultan Hassanal Bolkiah wanda ya bada umurnin fara aiki da dokokin shari’ar Musuluncin a ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu bayan tsaikon da aka samu na tsawon shekaru.

Hakazalika za a yi wa duk matar da aka samu da laifin tarawa da mace ‘yar uwarta bulala 40 ko kuma daurin shekaru 10 a gidan yari.

An fara wanzar da Shari'ar Musulunci a kasar Brunei

An fara wanzar da Shari'ar Musulunci a kasar Brunei
Source: UGC

KU KARANTA: El-Rufa'i ya yi arangama da masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja

Wasu sassan na dokokin, za su rika shafar hatta wadanda ba Musulmai ba, kamar mutumin da aka samu da laifin furta kalaman da ba su dace ba ga Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Sallam.

A jawabin da Sultan Bolkiah ya gabatar ga al’ummar kasar ta kafar talabijin, ya yi kira ga al'ummar kasar su bada kaimi wajen koyar da ilimin addinin Islama.

Sai dai tuni aka fara samun martani daga sassa daban daban na duniya, in da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana dokokin a matsayin zalunci da rashin tausayi, yayinda fitattun taurarin duniya karkashin jagorancin jarumin fina-finan nan, George Clooney da mawakin nan Elton John suka bukaci a kaurace wa otel-otel din da kasar ta Brunei ta mallaka a kasashen ketare kamar a Amurka da Turai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel