Muna wankin koda kyauta ga yan asalin jihar Yobe – Babban likita

Muna wankin koda kyauta ga yan asalin jihar Yobe – Babban likita

Babban Darektan likitoci na asibitin koyarwa dake jami’ar Yobe, Damaturu, Dr. Baba Waru Goni, ya ce asibitinsu ta fara gudanar da aikin wanke koda ga yan asalin jihar a kyauta kamar yanda gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam ya ba da umurni.

A wata hira da Jaridar Daily trust a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu a Damaturu, babban Darektan yace an soma bin umurnin ne tun daga watan Janairu 2019 bisa koke-koken cewa marasa lafiya na fama da tsadar farashin aikin wanke kodan duk da umurnin da gwamnan ya bayar.

Ya bayyana cewa a cikin watanni uku, anyi rijistan yan Yobe 103 wadanda ke fama da lallurar koda kuma asibitin ta gudanar da aikin wanke koda kusan sau 100 ga masu lalluran.

Goni yace kafin gudanar da aikin kyauta, an aika kwamiti jihar Katsina don koyon aiki daga kwararru da suka shafe shekaru 17 suna aikin don tabbatar da cigaban shirin a Yobe.

Muna wankin koda kyauta ga yan asalin jihar – Babban likitan asibitin Yobe
Muna wankin koda kyauta ga yan asalin jihar – Babban likitan asibitin Yobe
Asali: Depositphotos

Ya yi bayanin cewa gwamnatin jihar ta kuma amince da tura wata tawaga daga asibitin zuwa Mansura da ke Masar domin kulla yarjejeniya akan shirin dashen koda ga marasa lafiya a jihar.

KU KARANTA KUMA: Zaben Rivers: Wike na gaba da sama da kuri’u 290,000 yayinda INEC ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi 15

Ya bayyana cewa cibiyar kiwon lafiya a jihar ta kaddamar da kwamitin fasaha don bincike akan tushen abunda ke haddasa lallurar koda mai tsanani, wanda ke shafan al’umman yankin Arewacin jihar.

Yace kwamitin na dauke da sashin kiwon lafiyar al’umma, ma’aikatar kiwon lafiya na Tarayya, cibiyar kiwon Lafiya na duniya (WHO), cibiyar kula da cututtuka na Najeriya, inda ya kara da cewa sashi daga jami’ar Maiduguri da jami’ar Ahmadu Bello Zaria sun kasance cikin binciken don magance matsalar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel