Zamu mayar da dajin Sambisa ya zamo wajen tarihi da yawon bude ido - Rundunar soji

Zamu mayar da dajin Sambisa ya zamo wajen tarihi da yawon bude ido - Rundunar soji

- Rundunar soji ta ce za a mayar da dajin Sambisa ya zamo wajen yawon bude ido da kuma wata cibiya ta sanin tarihi

- Buratai ya ce cibiyar alkinta kayan yakin za ta jawo manyan masana da masu yawon bude ido zuwa dajin, da kuma kara samawa kasar kudaden shiga

- Taken taron bitar shi ne: "Bunkasa alakar da ke tsakanin rundunar soji da hukumar kula da wuraren yawon bude ido ta kasa: Mayar da hanali kan sha'anin tsaron kasar."

Rundunar soji ta ce za a mayar da dajin Sambisa ya zamo wajen yawon bude ido da kuma wata cibiya ta sanin tarihi, inda za a rinka alkinta kayayyakin yaki a shiyyar Arewa maso Gabas, domin baiwa masu yawon shakatawa damar ziyartar wajen.

Laftanal Janar Tukur Buratai, hafsan rundunar sojin kasa, ya bayyana hakan a wani taro da shelkwatar rundunar sojin ta shirya, kan "Dakile matsalolin tsaro da ke da alaka da dazuzzuka da kuma wuraren da aka killace su", wanda ya gudana a Abuja.

Buratai, wanda ya samu wakilcin Manjo Janar Ali Nani, shugaban tsare tsare, a yayin bude taron, ya ce cibiyar alkinta kayan yakin za ta jawo manyan masana da masu yawon bude ido zuwa dajin, da kuma kara samawa kasar kudaden shiga.

KARANTA WANNAN: Kasar Jamus ta taya shugaba Buhari murnar lashe zabe a karo na biyu

Zamu mayar da dajin Sambisa ya zamo wajen tarihi da yawon bude ido - Rundunar soji
Zamu mayar da dajin Sambisa ya zamo wajen tarihi da yawon bude ido - Rundunar soji
Asali: Twitter

Taken taron bitar shi ne: "Bunkasa alakar da ke tsakanin rundunar soji da hukumar kula da wuraren yawon bude ido ta kasa: Mayar da hankali kan sha'anin tsaron kasar."

Dr. Agboola Okeyoyin, mataimakin babban shugaban hukumar kula da wuraren yawon bude ido ta kasa, a yayin da ya ke gabatar da makalarsa mai taken: "Alkinta wuraren da aka killace da kuma tsaron kasa", ya ce da yawan dazuzzukan kasar sun koma mabuyar 'yan ta'adda.

A cewar sa, bangarorin da hukumar tare da hadin guiwar rundunar sojin suke son mayar da hankali akansu sun hada da gina cibiyar yawon bude ido ta kasa da kasa, cibiyar kula da dabobbi da sauran namun jeji, cibiyar kimiyyar alkinta muhimman abubuwan da suke cikin dajin.

A cewarsa, manyan wuraren da hukumar ke kula da su sun hada da manyan wuraren shakatawa guda bakwai, gidajen ajiye dabbobi guda 30, mabuyar dabbobin da ke cikin hatsari guda hudu da dai sauransu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel