Shaidan ne yayi mani muguwar huduba na rika afkawa Yara – Inji Fasto

Shaidan ne yayi mani muguwar huduba na rika afkawa Yara – Inji Fasto

Mun samu labari cewa babban Limamin nan na cocin Jesus Intervention Household Ministry, watau Prince Ezuma Chizemdere, ya shiga hannun hukuma bayan an kama sa yana lalata da yara maza.

Rabaren Prince Ezuma Chizemdere, yace shaidan ne yayi masa wasu-wasi har ta kai ya rika afkawa kananan yara a Unguwar Ejigbo da ke cikin Garin Legas. Yanzu haka wannan Fasto ya gogawa wasu cikin yaran cutar kanjamau.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa daya daga cikin Yaran da su ka fada cikin gonar wannan mugun mutumi, ya kamu da cutar Sida watau Kanjamau. Sunan wannan Matashi mai shekaru 16 da haihuwa a Duniya, Anthony Shedrack.

Jaridar tace tuni dai Matar wannan Fasto ta tsere ta bar sa bayan ta gano cewa Mijin da ta ke zama da shi yana bin yara Maza. Wannan fasto ya kan nemi Kananan yara ne ‘yan shekara 15 ko 16, inda yake saduwa da su, yana ba su kudi.

KU KARANTA: Ba a sace kowa a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ba - 'Yan Sanda

Daya daga cikin yaran da su ka shiga tarkon wannan Malami ne ya fadawa Iyayen sa abin da yake faruwa, a haka ne dai asirin sa ya tonu a hannun ‘yan sanda. Yaron yace wannan Limamin coci yana ba su N2, 000 ne idan yayi amfani da su.

Jami’an tsaro sun yi nasarar cafke Fasto Prince Chizemdere bayan an dauki tsawon lokaci ana neman sa a gidan sa da ke Unguwar Ejigbo. Bincike ya nuna cewa wannan Fasto ya tara yara ne har kusan su 15 yana saduwa da su ta dubura.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Vanguard, a duk rana ta Allah, wannan Limami ya kan wanke rigunan gadon barci a duk lokacin da ya shigo da Matasan da yake kwana da su a cikin gidan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel