Yawan cin kifi zai iya magance kamuwa da cutar asma - Bnciken masana

Yawan cin kifi zai iya magance kamuwa da cutar asma - Bnciken masana

- Wani masanin kimiyya daga Australia ya ce sun gano cewa yawaita cin kifi zai taimaka wajen magance kamuwa da cutar asma

- Farfesa Lopata ya ce bincike ya bayyana cewa canjin abinci da ake samu a fadin duniyar na daga cikin dalilan da ke haddasa yaduwar cutar asma

- Ya ce akwai karuwar cin sinadarin n-6 Polyunsaturated Fatty Acid (PUFA) wanda aka fi samunshi a jikin man ganye da kuma raguwar cin sinadarin n-3 PUPA

Wani masanin kimiyya daga jami'ar James Cook da ke kasar Australia ya ce binciken da suka gudanar ya bayyana wata sabuwar hanya da ta tabbatar da cewa yawaita cin kifi zai taimaka wajen magance kamuwa da cutar asma.

Farfesa Andreas Lopata daga JCU, tsangayar bincike da nazarin kiwon lafiya da magunguna ta Australia (AITHM) ya shiga cikin masu binciken wanda ya gwada mutane 642 wadanda ke aiki a ma'aikatar sarrafa kifaye da ke a wani karamin kauye a cikin kudancin Afrika.

"Kusan mutane 334m ne a duniya ke fama da cutar asma, kuma akalla kashi daya cikin hudu na mutane miliyan daya ke mutuwa daga cutar a kowacce shekara. A kasar Australia, kashi daya daga cikin 9 na mutane kasar na fama da cutar asma (akalla mutane miliyan 2.7)."

KARANTA WANNAN: Yanzunnan: Yan kungiyar asiri sun katse rayuwar dalibi da masu bautar kasa 2 a Bayelsa

Yawan cin kifi zai iya magance kamuwa da cutar asma - Bnciken masana
Yawan cin kifi zai iya magance kamuwa da cutar asma - Bnciken masana
Asali: UGC

Farfesa Lopata ya ce a tsarin da ake ciki yanzu, bincike ya bayyana cewa canjin abinci da ake samu a fadin duniyar na daga cikin dalilan da ke haddasa yaduwar cutar asma.

"Akwai karuwar cin wani sinadari da aka fi sani da n-6 Polyunsaturated Fatty Acid (PUFA) wanda aka fi samunshi a jikin man ganye da kuma raguwar cin sinadarin da aka fi sani da n-3 PUPA, wanda aka fi samunsa a man kayan ruwa. Tabbas an samu karanci daga amfani da sabon kifi, inda aka zafi amfani da wanda aka sarrafa," a cewarsa.

Farfesa Lopata ya ce an zabi kauyen ne domin gudanar da binciken akansu saboda kasancewar al'ummar garin sunfi amfani da sabon kifi kuma suna da karancin ababen more rayuwa, wannan ya kara tabbatar da cewa za a fi samun man marin daga kifi da kuma sauran kayan ruwa, kasancewar suna da sinadarin n-3.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel