Majalisar dattawa ta dage zamanta kan mutuwar dan majalisa

Majalisar dattawa ta dage zamanta kan mutuwar dan majalisa

- Majalisar dattawa a ranar Talata, 12 ga watan Maris ta dage zaman majalisar domin karrama wani mamba na majalisar wakilai, Hon. Temitope Olatoye

- Yan bindiga ne suka kashe Olatoye a lokacin zaben gwamna da na yan majalisar jiha wanda ya gudana a ranar Asabar da ya gabata

- Majalisar za ta dawo zama a ranar Laraba domin ci gaba da muhawara kan kasafin kudin 2019

Majalisar dattawa a ranar Talata, 12 ga watan Maris ta dage zaman majalisar domin karrama wani mamba na majalisar wakilai, Hon. Temitope Olatoye, wanda ya rasa ransa a lokacin zaben gwamna da na majalisar dokokin jiha da ya gudana a Ibadan, babbar birnin jihar Oyo.

Majalisar ta dawo zama ne da misalin karfe 10.50 na safe inda Shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ya bude taro da addu’a kafin ya karanto zaman majalisar na karshe na ranar 26 ga watan Fabrairu.

Majalisar dattawa ta dage zamanta kan mutuwar dan majalisa
Majalisar dattawa ta dage zamanta kan mutuwar dan majalisa
Asali: Twitter

An gabatar da bayanan zaman karshen lokacin da Shugaban masu rinjaye a majalisar, Sanata AhmadLawan ya zo karkashin oda ta 43 ya sanar da mutuwar dan majalisar sannan ya nemi a karrama shi ta hanyar yin shiru na minti daya.

Ya kuma nemi a dage zaman majalisar kamar yadda yake a al’adar majalisar dokokin kasar domin karra,a marigayi dan majalisar.

KU KARANTA KUMA: Zabe: Ya zama dole ku kare hakki da ra’ayin yan kasa – Shugaban Alkalan Najeriya ga Alkalai

Sai aka amsa bukatar Lawan sannan aka dage zaman zuwa ranar Laraba domin fara muhawara akan kasaafin kudin 2019.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel