Sakamakon Zabe: Ganduje ya yi nasara a kananan hukumomi 3 na jihar Kano
A yayin da hukumar zabe da kasa mai zaman kanta ta fara bayyana sakamakon zaben gwamnoni da 'yan majalisun dokoki da aka gudanar a jiya Asabar, 9 ga watan Maris, mun samu cewa, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi nasara cikin wasu kananan hukumomi uku na jihar.
Cikin sakamakon kananan hukumomi hudu da hukumar INEC ta wassafa sakamakon su a yau Lahadi, mun samu cewa, gwamna Abdullahi Ganduje ya yi nasara cikin uku daga cikin su kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.
Kananan hukumomin hudu na jihar Kano da hukumar INEC ta bayyana sakamakon su kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito sun hadar da; Albasu, Bebeji, Karaye da kuma karamar hukumar Bunkure.
KARANTA KUMA: Sakamakon Zabe: Hukumar 'yan sanda ta gargadi al'umma kan gudanar da bikin murna a jihar Kano
Turawan zaben na kananan hukumomin Albasu, Farfesa Mustapha Hassan Bichi, karamar hukumar Bunkure, Farfesa Nuruddeen Magaji da kuma na karamar hukumar Karaye, Farfesa Bello Idris Tijjani, sun tabbatar da nasarar dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar APC da ya kasance Gwamna Ganduje.
Sai dai Gwamna Ganduje cikin karamar hukumar Bebeji, ya sha kasa a hannun abokin adawar sa na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf kamar yadda Baturen zabe Farfesa Ibrahim Barde ya bayyana.
Ga yadda sakamakon zaben ya kaya cikin kananan hukumomin hudu tsakanin Ganduje da Abba kamar yadda hukumar INEC ta zayyana.
Karamar Hukumar Albasu
APC: 25,358
PDP: 18,401
Karamar Hukumar Bunkure
APC: 20,271
PDP: 19,932
Karamar Hukumar Karaye
APC: 18,770
PDP: 17,163
Karamar Hukumar Bebeji
PDP: 18,533
APC: 17,418
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng