Har yanzu nine dan takarar gwamnan PDP a Kano - Abba Kabir Yusuf

Har yanzu nine dan takarar gwamnan PDP a Kano - Abba Kabir Yusuf

- Abba Kabir Yusuf yace har yanzu shine dan takarar gwamnan PDP a Kano

- Hakan ya biyo bayan umurnin da kotu ta saki a ranar Litinin, 4 ga watan Maris cewa an soke takarar Injiniya Abba a matsayin dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Kano

Biyo bayan umurnin da kotu ta saki a ranar Litinin, 4 ga watan Maris cewa an soke takarar Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamna a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kano, dan takarar na PDP ya bayyana cewa umurnin bai shafi takararsa ba kamar yadda shari’an ke akan PDP ne, wanda a cewarsa jam’iyyar ta dauki matakin da ya kamata na rook domin maganace lamarin.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin dan takarar na PDP a Kano, Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa.

Har yanzu nine dan takarar gwamnan PDP a Kano - Abba Kabir Yusuf
Har yanzu nine dan takarar gwamnan PDP a Kano - Abba Kabir Yusuf
Asali: UGC

A cewar jawabin, abunda dan takarar ya sani shine cewa, zai ci gaba da gudanar da ayyukan kamfen dinsa har zuwa daren ranar Alhamis lokacin da wa’adin kamfen din zai kare kamar yadda yake a dokar zaben 2010.

An kuma zargi jam’iyyar APC mai mulki da kasancewa umulabaisin wannan lamari duk don su jikata babbar jam’iyyar adawa kafin zaben ranar Asabar saboda tsaoron da suke ji.

KU KARANTA KUMA: Ana gab da zaben gwamna: El-Rufai ya tarbi mambobin PDP 30,000 a Kaduna

Sun kuma yi kira ga dukkanin mambobin PDP da tawagar magoya bayan Injiniya Abba Kabir Yusuf da su kwantar da hankalinsu sannan su ci gaba da shirin kamfen dinsu domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a aben ranar Asabar, 9 ga watan Maris mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel