Mutanen Kano sun dade suna bani goyon baya tun a 2003 - Buhari

Mutanen Kano sun dade suna bani goyon baya tun a 2003 - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Kano ce cibiyar siyasarsa tun bayan da ya shiga harkar siyasar Najeriya a 2003.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa Kano ta dade tana bashi goyon baya ko a lokacin da bai yi nasara ba.

Zababben shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da wata tawaga daga kudancin Kano suka kai masa ziyarar taya murna a Abuja.

Mutanen Kano sun dade suna bani goyon baya tun a 2003 - Buhari
Mutanen Kano sun dade suna bani goyon baya tun a 2003 - Buhari
Asali: Depositphotos

Shugaba Buhari ya bayyana cewa ba zai iya godema mutanen Kano ba akan tsayawa da suka yi tare dashi a lokaci dadi da wuya. Ya nuna jin dadi akan goyon bayansa da suka yi da kuma addu’o’insu a gare shi.

Buhari ya kuma yi godiya ga Sanata Kabiru Ibrahim Gaya kan goyon bayansa inda ya kara da cewa kokarinsa a matsayin Shugaban kwamitin aiki na majalisar dattawa ta kawo ci gaba sosaiu a gwamnatinsa tsawon shekaru hudu da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: Idan akwai ‘Yan takaran da su ka fi ‘Yan Jam’iyyar APC kyau, ku zabe su – Inji Buhari

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren ranar Asabar da ya gabata ya yi bayanin cewa Najeriya ta dauki lokaci kafin ta gyaru saboda tsawon lokacin da tsohuwar gwamnatin Peoples Democratic Party ta bata tana mulki na tsawon shekaru 16.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da uwargidan Shugaban kasar Aisha Buhari ta ba mata da matasa tabbacin samun gurbi gwamnatin Buhariu na biyu, cewa Shugaban kasar zai dinke barakar da ke tsakanin masu kudi da talaka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel