Da dumin sa: 'Yan bindiga sun kai wani mummunan farmaki a Zamfara, sun kashe mutane

Da dumin sa: 'Yan bindiga sun kai wani mummunan farmaki a Zamfara, sun kashe mutane

Wasu sabbin rahotanni da muka samu daga majiyoyin mu sun bamu labarin cewa akalla mutane 30 ne suka rasa ransu a wani sabon hari da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai a garin kwari da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.

Majiyar ta mu ta ambato wani daga cikin wadanda rikicin ya rutsa da su mai suna Dakta Suleiman Shu'aibu Shinkafi yana cewa lamarin ya faru ne a ranar kasuwar Shinkafi, a daidai lokacin da jami'an sa-kai suke kokarin raka jama'a domin cin kasuwa.

Da dumin sa: 'Yan bindiga sun kai wani mummunan farmaki a Zamfara, sun kashe mutane
Da dumin sa: 'Yan bindiga sun kai wani mummunan farmaki a Zamfara, sun kashe mutane
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ganin karshen rikicin Zamfara ba yanzu ba - Gwamna Yari

Legit.ng Hausa ta samu cewa Dakta Suleiman ya shaidawa majiyar mu cewa a ranar kasuwar, barayin sun bude wa jami'an sa-kai da kuma 'yan kasuwar wuta inda suka kashe su gaba daya.

Haka zalika ma ya koka bisa rashin tsaron da suke fama da shi a wannan yankin na Shinkafi, inda ya bayyana cewa akwai karancin sojoji da 'yan sanda, kuma jami'an sa-kai ne "suke taimaka wa jama'a a wannan yankin."

Da kuma aka tuntubi kakakin 'yan sanda na jihar, inda ya tabbatar da faruwar lamarin amma babu wani cikakken bayani a kan adadin mutanen da suka mutu ko kuma jikkata. Sai dai kakakin 'yan sandan ya ce suna gudanar da bincike kuma za su yi karin bayani idan sun kammala.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel