Wani dan Najeriya ya cika alkawarin da ya dauka na shiga kwata idan Buhari yayi nasara (hoto)

Wani dan Najeriya ya cika alkawarin da ya dauka na shiga kwata idan Buhari yayi nasara (hoto)

A ranar 23 ga watan Fabrairu, yan Najeriya da dama sun fita sun kada kuri’unsu a lokacin zaben Shugaban kasa a yankuna daban-daban na kasar.

Sai dai yan kwanakin da suka biyo baya mutane sun kasance cikin zullimi yayinda suke jiran sakamakon zaben. Bayan kwanaki hudu ana abu daya sai sakamakon zaben ya fito sannan aka kaddamar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasar.

Sanar da sakamakon ya haifar da martini daban-daban masu ban al’ajab i daga wajen wasu mutane.

Legit.ng ta tattaro rahoton wani matashin mutum wanda ya nuna farin ciki da sakamakon zaben harma ya cika wani alkawari da ya dauka mai ban mamaki.

Mutumin wanda ke da zama a Bauchi ya yi alkawarin tsoma kanshi a cikin kwata na tsawon mintuna 10 idan Buhari yayi nasarar zabe.

KU KARANTA KUMA: An samu matsala: Manyan kwamishinoni a hukumar INEC zasu yi murabus

A yanzu ya cika alkawarinsa yayinda aka bayyana hoton dage da hannu da alamar 4 + 4 bayan ya fito daga kwatan.

Kalli hotonsa a kasa:

Wani dan Najeriya ya cika alkawarin da ya dauka na shiga kwata idan Buhari yayi nasara (hoto)
Wani dan Najeriya ya cika alkawarin da ya dauka na shiga kwata idan Buhari yayi nasara
Asali: UGC

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta tattaro cewa daya daga cikin magoya bayan Shugaban kasar kuma jarumar Kannywood, Sadiya Kabala ta je shafin zumunta inda ta nuna farin ciki yayinda ta fashe da kukan murna akan nasarar da Shugaban kasar ya samu a zaben.

A bidiyon wanda kakakin kungiyar kamfen din Shugaban kasa na APC, Festus Keyamo (SAN) ya wallafa, an gano Sadiya tana yiwa Buhari barka da samun nasara sannan ta yi godiya ga Allah da ya ba Shugaban kasar Nasara yayinda take hawaye idanu bibbiyu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel