Sakamakon zaben 2019: Kashim Shettima ya zama sanata

Sakamakon zaben 2019: Kashim Shettima ya zama sanata

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Kasa INEC ta sanar da cewa Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Borno ne ya lashe zaben sanata na mazabar Borno ta Tsakiya.

A yayin da ya ke bayyana sakamakon zaben a ranar Talata a Maiduguri, bataren zabe na jihar Farfesa Yusuf Yusuf ya ce Shettima ne ya lashe zaben da kuri'u 342,898 a zaben da akayi ranar Asabar yayin da abokin hammayarsa na jam'iyyar PDP ya zo na biyu da kuri'u 75,506.

Shettima zai maye gurbin Babakaka Bashir a majalisar tarayya.

DUBA WANNAN: Kin amincewa da sakamakon zabe: INEC ta mayarwa PDP martani

Kashim Shettima ya zama sanata
Kashim Shettima ya zama sanata
Asali: Depositphotos

Mazabar Borno ta Tsakiya ta kunshi mazabu takwas ne da suka hada da Maiduguri, Jere, Konduga da Bama.

Sauran sune Mafa, Dikwa, Ngala da Kala Balge.

Kazalika, Abdulkadir Rahis na jam'iyyar APC ya lashe zaben dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Maiduguri.

Bataren zabe na jihar, Farfesa Aminu Ayuba ya bayyana cewa Rahis ya yi nasara ne da kuri'u 93.497 inda ya kayar da Abdulsalam Kachalla na jam'iyyar PDP da ya samu kuri'u 60,132.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa ana sa ran bayyana sakamakon zaben shugaban kasa a nan gaba idan an kammala tattara sakamakon zabe daga jihohi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel