Yanzu-yanzu: Sace akwatin zabe: Buhari ya shiga ganawar gaggawa da Buratai, gwamnoni da manya hafsoshin tsaro

Yanzu-yanzu: Sace akwatin zabe: Buhari ya shiga ganawar gaggawa da Buratai, gwamnoni da manya hafsoshin tsaro

Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar gaggawa da manyan hafsoshi tsaron Najeriya, sifeton yan sanda, Mohammed Adamu, da wasu gwamnonin arewacin Najeriya a ranan Talata, 19 ga watan Febrairu, 2019.

An fara ganawar ne misalin karfe 11 na safe a ofishin shugaban kasa.

Manyan hafsoshi tsaron dake hallare sune babban hafsan hukumar tsaro, Janar Gabriel Olonisakin; babban hafsan sojin sama, Air MArshal Abubakar Sadique, Janar Tukur Buratai; IGP Mohammed Adamu.

Gwamnonin da ke halarce a taron sune gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow; gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima; da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

Sauran ma'aikatan gwamnatin ke cikin ganawar sune shugaban ma'aikatan Buhari, Abba Kyari; ministan tsaro, Masur Dan Ali; da ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Danbazzau.

An cikin ganawar yayinda muka kawo wannan rahoto.

KU KARANTA: Sheikh Daurawa ya jagoranci malamai sama da 100 zuwa yiwa Kwankwaso mubayi'a a Kano

Wannan ya biyo bayan jawabin hukumar sojin Najeriya inda ta dauki alwashin cika umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari daya bayar na bindige duk wani ko wasu da aka kama suna kokarin sace akwatin zabe a babban zaben kasar da zai gudana a mako mai zuwa.

A ranar Litinin ne shugaba Buhari ya bada wannan umarni yayin wani taron jam’iyyar APC na musamman daya gudana a babban ofishin jam’iyyar na kasa dake babban birnin tarayya a Abuja, sai dai batun ya janyo cecekuce a tsakanin yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel