Zaben 2019: Kungiyar yan darikar Tijjaniyya ta umurci mabiyanta su zabi Buhari

Zaben 2019: Kungiyar yan darikar Tijjaniyya ta umurci mabiyanta su zabi Buhari

Kungiyar sufaye na darikar Tijjaniyya ta Najeriya ta umurci mabiyanta a fadin tarayya da su zabi shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben da zai gudana ranan Asabar, 16 ga wtaan Febrairu, 2019.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a watan jawabin da shugaban kungiyar SUFI, Timasaniyu Ahmed Rufai ya saki inda yace kungiyar ta yi ittifaki a yi Buhari saboda an gwadashi kuma an gani, saboda haka za'a iya amincewa da shi.

A Jawabin, ya lissafa wasu ayyuka da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tayi wajen gyara kasa, yaki da cin hanci, farfado da tattalin arziki da sauransu.

Yace: "Yaki da cin da rashawa na kankama. Wadanda suke ganin ba za'a iya tabasu ba suna ji ba dadi yanzu, ana samun nasarar gurfanar dasu kuma wasu daga cikinsu na gidan yari. Da yawa kuma sun gudu daga kasar da suka taba shugabanta."

"Rashawa cuta ce kuma ya zama wajibi mu hada kai da shugaba Muhammadu Buhari wajen yakanta."

Bisa ga wannan dalili da kuma bukatan cigaba kan nasarorin da shugaba Muhammadu Buhari ya samu, mu mabiya Tijjaniya SUFI a fadin tarayya mun alanta goyon bayanmu ga shugaba Buhari a zaben 16 ga febrairu, 2019."

Kana muna kira ga dukkan yan Najeriya da mu kada kuri'unmu ga shugaban kasa domin rana goben kasar nan da kuma yaranmu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel