Maza kwaya, mata kwaya: An tura wani kwamishinan Yansanda mai abin mamaki jahar Kano

Maza kwaya, mata kwaya: An tura wani kwamishinan Yansanda mai abin mamaki jahar Kano

Babban sufetan Yansanda, Mohammed Adamu ya tura shahararren jami’in Dansandan nan, Mohammed Wakili a matsayin sabon kwamishinan Yansandan jahar Kano kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Wakili yayi suna ne tun bayan bayyana wani faifan bidiyonsa a shafukan sadarwar zamani, inda yake magana akan yawaitar shaye shaye a tsakanin matasan jahar Katsina, jahar da yake rike da mukamin kwamishina a baya.

KU KARANTA; Ganduje ya bude ma Atiku dandanlin da zai gudanar da gangamin yakin neman zabe

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Wakili ya gaji tsohon kwamishinan Yansandan jahar Kano, Rabiu Yusuf, kuma yana daga cikin Yansandan da suka fara aiki a hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, a yanzu dai sauranshi watanni 3 ya yi murabus.

Dalilin daya janyo ma Wakili shahara shine yadda yake magana irin ta mashaya a yayin da yake kokawa akan halayyar matasa na yawan shaye shaye tare da ta’ammali da miyagun kwayoyi, inda yace;

“Shaye shayen yayi yawa a ko ina, duk inda kaje shaye shaye, kowa na kokawa akan ta’ammali da miyagun kwayoyi, Maza kwaya, Mata kwaya, Manya kwaya, Yara ma kwaya.” Inji shi, yana yi yana rangaji da kai.

Idan za’a tuna jahar Kano na daga cikin jihohin da akafi samun yawaitan matsalar shaye shaye tsakanin al’ummarta, inda ko a ranar Litinin data gabata sai da hukumar yaki da sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi, NDLEA, ta kai same same a wuraren shaye shaye 35 a cikin garin Kano.

Kwamandan rundunar, Ibrahim Abdul ne ya bayyana haka, inda yace wuraren sun hada da “Plaza, Sanya Olu, Kabuga, Rimin Kebe, Danzaki , Sauna, Warure, Aisami, Sabon Titi, Dorayi, Hauren Gadagi, tashar Kwanar Dan-marke, Chalawa, Madobi, titin Ring rod, Farawa, tashar Mariri da Kofar Ruwa.”

Sai dai majiyoyi daga hukumar Yansandan jahar sun tabbatar da cewa sabon kwamishinan Yansanda, Mohammed Wakili na da kwarewar da zai yaki matsalar shaye shaye a jahar Kano gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel