Mu leka kotu: Wata mahaifiya ta bukaci a maidawa diyarta 'yar shekaru 4 budurcinta

Mu leka kotu: Wata mahaifiya ta bukaci a maidawa diyarta 'yar shekaru 4 budurcinta

- Al'ummar da ke zaune a Osogbo, jihar Osun sun kasance cikin dimauta a lokacin da wani direban motar dalibai ya ya yi lalata da wata daliba mai shekaru 4

- Kotun lardi da ke da zama a babban birnin jihar, ta ki bayar da belin wanda ake zargin kasancewar laifin da ake zarginsa da aikata na da girman gaske

- Sai dai, mahaifiyar yarinyar ta ce ba zata iya hakura ba har sai idan za a iya mayarwa diyarta da budurcinta da ta rasa, inda kuma ta bukaci gwamnati ta sanya baki domin ayi mata adalci

Al'ummar da ke zaune a Osogbo, jihar Osun sun kasance cikin dimauta a ranar Talata, 16 ga watan Janairu, 2019, a lokacin da wani direban motar daliban wata makaranta mai zaman kanta, Oluwatomisin Oyelakin mai shekaru 28, ya yi lalata da wata daliba, wacce ba a bayyana sunanta ba.

Kotun lardi da ke da zama a babban birnin jihar, ta bayar da umurnin garkame wanda ake zargin har sai ranar 28 ga watan Fabreru, 2019, a lokacin da zata sake sauraron karar da kuma duba bukatar da aka gabatar na bayar da belinsa, kasancewar laifin da ake zarginsa da aikata na da girman gaske.

Mahaifiyar 'yar karamar yarinyar, wacce ta koka ga mahukunta da su yi adalci akan wannan mummunan aika-aikatan da direban yayiwa diyarta, wacce ya sa ta rasa budurcinta a wannan gabar da take da shekaru 4 kacal a duniya.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Amurka, Birtaniya da EU sun yi tsokaci kan dakatar da Onnoghen

Mu leka kotu: Wata mahaifiya ta bukaci a maidawa diyarta 'yar shekaru 4 budurcinta
Mu leka kotu: Wata mahaifiya ta bukaci a maidawa diyarta 'yar shekaru 4 budurcinta
Asali: Twitter

Binciken da jami'an tsaro suka gudanar ya bayyana cewa direban da ake zargin ya yi mata fyade ne kasa da awanni 48 da sanyata makarantar, mai suna Charleston Groups of School, da ke yankin Kelebe, cikin garin Osogbo.

Rahotanni sun bayyana cewa a halin yanzu yarinyar na karkashin kulawar likitoci na musamman, saboda karfin da aka yi amfani da shi wajen kutsawa cikin farjinta wanda kuma yayi sanadin rasa budurcinta, kamar yadda jami'an rundunar 'yan sanda suka tabbatar a asibitin 'yan sanda da ke Osogbo.

Bayan gurfanar da wanda ake zargin, rahotanni sun bayyana cewa mahukuntan makarantar sun ci gaba da yin matsin lamba ga mahaifiyar yarinyar akan su sasanta lamarin ba tare da zuwa kotu ba, kasancewar mai makarantar babban dan takara ne a zabe mai zuwa, hakan na iya lalata kudurinsa na cin zabe, da zummar cewa za biyata ko nawa take so.

Sai dai, a cewar rahotannin, mahaifiyar taki amincewa da wannan bukata ta mahukuntan makarantar, inda tace zata iya yafewa ne akan sharadi daya, sharadin kuwa shine idan har zasu iya mayarwa diyarta da budurcinta da ta rasa, inda kuma ta bukaci gwamnati ta sanya baki domin ayi mata adalci.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.n

Asali: Legit.ng

Online view pixel