Inna Lillahi wa inna ilayhi raji'un: Allah ya yiwa Gaji Galtimari na jihar Borno rasuwa

Inna Lillahi wa inna ilayhi raji'un: Allah ya yiwa Gaji Galtimari na jihar Borno rasuwa

Labarin da Legit.ng ta samu yanzu, na nuni da cewa wani babban jigo a jihar Borno kuma tsohon jakadan Nigeria a kasar Chad, Gaji Galtimari, ya rasu. Ya rasu ne a daren ranar Asabar a Maiduguri, yana da shekaru 81 a duniya, bayan da ya sha fama da lalurar rashin lafiya.

An yiwa Gaji Galtimari sutura a Maiduguri kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar bayan da babban limamin Borno ya jagoranci yi ma gawarsa jana'iza, inda gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya halarta.

Mr Galtimari dai shine shugaban kungiyar dattawan Borno kuma shugaban kungiyar al'ada ta Kanem Borno.

KARANTA WANNAN: Fatattakar 'yan ta'adda: Rundunar sojin sama ta tura jirgin yakin sama da dakaru zuwa Sokoto

Inna Lillahi wa inna ilayhi raji'un: Allah ya yiwa Gaji Galtimari na jihar Borno rasuwa
Inna Lillahi wa inna ilayhi raji'un: Allah ya yiwa Gaji Galtimari na jihar Borno rasuwa
Asali: Twitter

Kafin rasuwarsa, Mr Galtimari ya yi aikin gwamnati inda har ya rike mukamin babban sakatare kafin daga bisani aka nadashi sakatre a gwamnatin soji na jihar Borno karkashin Abdulmuminu Aminu. Daga baya ne kuma aka nada shi jakadan Nigeria a kasar Chadi a lokacin gwamnatin soji ta Ibrahim Badamasi Babangida.

Mukamin karshe da ya rike kafin mutuwarshi shine shugaban kungiyar al'adu da tarihi ta Kanem Borno, wacce a makon da ya gabata ta gudanar da bukin kaddamar da wani littafinta na farko kan tarihin daular Kanem Borno, mai taken 'Kanem Borno: 'A Thousand Years of Heritage'.

Haka zalika yana da cikin na gaba gaba a wani yunkuri da gwamnatin tarayya tayi na kulla yarjejeniya da 'yan ta'addan Boko Haram wanda daga baya yaci tura.

Ya rasu ya bar 'yaya da jikoki da dama.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel