2019: Ka daina muzgunawa Abokan hamayya – Amurka ta fadawa Buhari

2019: Ka daina muzgunawa Abokan hamayya – Amurka ta fadawa Buhari

Mun ji labari cewa Kasar Amurka ta fara gargadin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan babban zaben da yake shirin gabatowa a fadin Najeriya nan da kusan kasa da makonni 4 masu zuwa.

2019: Ka daina muzgunawa Abokan hamayya – Amurka ta fadawa Buhari
Jami’an majalisar kasar Amurka sun yi magana kan zaben 2019
Asali: Depositphotos

Majalisar kasar Amurka tagargadi shugaba Muhammadu Buhari ya daina kokarin hana ‘yan adawa sakat a Najeriya a daidai lokacin da zabe ke gabatowa. Hakan na zuwa ne bayan rade-radin yunkurin binciken Atiku Abubakar.

Amurka ta cin ma wannan matsaya ne bayan wani zama da majalisar ta tayi kwanan nan inda ta fitar da jawabi cewa gwamnatin Najeriya ta shafawa manyan ‘yan adawa lafiya a daidai wannan yanayi da ake shirin yin zabe a kasar.

Wani babban jami’in majalisar wakilan tarayyar Amurka mai suna Zachary Seidl, sh ne ya bayyawa jaridar This Day ta Najeriya wannan. Siedl ya nemi ayi zabe na kwarai da adalci a watan gobe ba tare da yin magudi ko kuma murdiya ba.

KU KARANTA: An hurowa APC wuta ta dakatar da wani Gwamnan ta mai shirin barin gado

Wasu ‘yan majalisa da ke lura da sha’anin kasashen Afrika ne su ka fara kawo wannan batu a Ranar Laraba. Daga cikin ‘yan wadannan kwamiti a majalisar Amurkan akwai Karen Bass, Elliot L. Engel, Chris Smith, Steve Chabot da sauran su.

Majalisar ta bakin C. Smith tace zaben Najeriya yana da muhimmanci a kaf yankin Afrika don haka dole Buhari yayi kokari wajen ganin an daina muzugunawa ‘yan adawa da kuma kashe jama’a a cikin tsakiyar Arewacin kasar.

Ana zargin Atiku Abubakar da laifi iri-iri a Najeriya, daga ciki har da zargin lashe wani tsohon banki na PHB. Babban Abokin hamayyar na Buhari ya karyata wannan inda ya nemi gwamnati ta fito da hujjojin ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel