'Yan sanda sun samu daurin gindin kotu a kan cigaba da tsare Dino Melaye

'Yan sanda sun samu daurin gindin kotu a kan cigaba da tsare Dino Melaye

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta samu izini daga Babban Kotun Abuja na cigaba da tsare Sanata Dino Melaye har na tsawon makonni biyu.

Sanarwar da ta fito daga bakin mai magana da yawun rundunar, DCP JImoh Moshood ya ce har yanzu ana bincikar Melaye kuma yana hannun 'yan sanda har na tsawon kwanaki 14 bayan izinin kotu da muka karba a ranar 9 ga atan Janairun 2019.

Ya ce, "ana binciken Melaye ne kan laifin hadin baki da yunkurin kisan kai da akayi a ranar 19 ga watan Yulin 2018 inda Melaye da 'yan dabarsa suka harbi Saja Danjuma Saliu a yayin da ya ke gudanar da aikinsa a hanyar Aiyetore Gbede, Mopa Road a jihar Kogi.

'Yan sanda sun samu izinin tsare Dino Melaye na kwanaki 14
'Yan sanda sun samu izinin tsare Dino Melaye na kwanaki 14
Asali: UGC

"Tawagar binciken na 'yan sanda ta nemi izinin tsare Dino Melaye na tsawon kwanaki 14 daga babban kotun Abuja a ranar 9 ga watan Janairun 2019 domin bincikar Sanatan kan zargin yunkurin kisan kai a ranar 23 ga watan Janairun 2019.

DUBA WANNAN: 'Yan majalisar dokoki 2 sun fita daga APC a Jigawa

"Dan sandan da suka harba, Saja Danjuma Saliu har yanzu bai gama warkewa ba daga raunin harsashin bindigan da suka harbe shi da ita.

"Zamu tabbatar da mun binciki Dino Melaye tare da sauran wadanda ake zargi da hannu cikin yunkurin kisar," inji Sanarwar 'yan sandan.

An kama Melaye ne a makon da ta gabata bayan 'yan sanda sun mamaye gidansa da ke Maitama Abuja na tsawon kwanaki 8.

Daga bisani an dauke shi daga asibitin 'yan sanda da ke Garki a Abuja zuwa asibitin 'yan sandan farar hula DSS a yammacin ranar Juma'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel