'Yan Sumoga sun salwantar da rayuwar jami'in Kwastam 1, sun raunata 1 a jihar Ogun

'Yan Sumoga sun salwantar da rayuwar jami'in Kwastam 1, sun raunata 1 a jihar Ogun

Hukumar hana fasakauri ta Najeriya reshen jihar Ogun, ta ce 'yan sumoga sun aikata mummunan ta'addanci na yiwa kasa fasadi kan wasu jami'an ta biyu yayin da suke tsaka da sintiri gami da ran gadi domin sauke nauyin da rataya a wuyan su.

Mun samu cewa, hukumar hana fasakauri ta Najeriya reshen jihar Ogun, ta ce mummunan ta'addanci da yiwa kasa fasadi na 'yan sumoga ya afkawa wasu jami'an ta biyu yayin da suke tsaka a bakin aiki.

Hukumar ta bayyana cewa, 'yan sumoga sun yiwa jami'an ta biyu kwanton bauna a ranar Lahadin da ta gabata inda suka salwantar da rayuwar jami'i guda tare da sassara dayan da adda ta saran itace.

'Yan Sumoga sun salwantar da rayuwar jami'in Kwastam 1, sun raunata 1 a jihar Ogun

'Yan Sumoga sun salwantar da rayuwar jami'in Kwastam 1, sun raunata 1 a jihar Ogun
Source: Depositphotos

Cikin sanarwar da kakakin reshen hukumar ya bayyana a yau Litinin, Abdullahi Aliyu Maiwada ya ce azal ta afkawa jami'an biyu bayan da suka datse wasu Motoci takwas dauke da buhunan shinkafa ta kasashen ketare da aka sulalo da su ta haramtacciyar hanya.

A yayin yunkurin karbe wannan ababe na fasaukauri, 'yan sumogon cikin shammace su ka farma jami'an biyu inda nan take jami'i guda, Hamisu Sani yace ga garin ku nan yayin da Tijjani John Michelle ya tsira da munanan raunuka na saran adda.

KARANTA KUMA: 2019: 'Yan Najeriya Miliyan 84 ke da rajistar zabe - INEC

Majiyar rahoton ta Sun News ta zayyana cewa, tuni aka gudanar da jana'izar jami'in da ya riga mu gidan gaskiya tare da binne shi a bisa tsari da kuma tanadi na shari'ar Musulci yayin da daya ke ci gaba da samun kulawa a gadon asibiti.

Tuni dai hukumar ta fara gudanar da binciken diddigi bayan ta cafke wasu mutane biyu da ake zargin hannun su cikin wannan mummunar ta'ada kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel