Hotunan ta'aziyyar da Shugaba Buhari ya kai jihar Sokoto

Hotunan ta'aziyyar da Shugaba Buhari ya kai jihar Sokoto

Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Sokoto daga domin kai gaisuwar ta'aziyya da iyalan tsohon shugaban kasan Najeriya, Alhaji Shehu Shagari da safiyar ranan Lahadi, 30 ga watan Disamba, 2018.

Shugaban kasan ya tashi daga babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe misalin karfe 9 na safe.

Hotunan ta'aziyyar da Shugaba Buhari ya kai jihar Sokoto

Hotunan ta'aziyyar da Shugaba Buhari ya kai jihar Sokoto
Source: Facebook

A Ranar Juma’a ne aka ji wani labari mai matukar ban takaici na rasuwar tsohon shugaban Alhaji Shehu Shagari. An binze Shehu Shagari ne a Jihar Sokoto a Ranar Asabar bayan ya rasu a yammacin Ranar Juma’a.

Hotunan ta'aziyyar da Shugaba Buhari ya kai jihar Sokoto

Hotunan ta'aziyyar da Shugaba Buhari ya kai jihar Sokoto
Source: Facebook

Jama’a da dama sun hallara wajen yi wa tsohon shugaban kasar na Najeriya sallar jana'iza. Sai dai shugaban kasa Muhammadu Buhari bai halarci taron jana’izar da aka yi a Garin na Sokoto ba. Shugaba Buhari ya aika wakili ne zuwa wurin.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari da mukarraban gwamnatin sa a wajen sallar da aka yi Shehu Shagari. Ko da dai Sakataren gwamnatin na Najeriya ba musulmi bane.

Hotunan ta'aziyyar da Shugaba Buhari ya kai jihar Sokoto

Hotunan ta'aziyyar da Shugaba Buhari ya kai jihar Sokoto
Source: Facebook

Hotunan ta'aziyyar da Shugaba Buhari ya kai jihar Sokoto

Hotunan ta'aziyyar da Shugaba Buhari ya kai jihar Sokoto
Source: Facebook

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel