Da duminsa: Rundunar 'yan sanda ta fara farautar Dino Melaye akan yunkurin kisan kai

Da duminsa: Rundunar 'yan sanda ta fara farautar Dino Melaye akan yunkurin kisan kai

- Rundunar 'yan sanda ta ce akwai wasu tambayoyi da take son Sanata Dino Melaye ya amsa a gabanta kan zargin da take masa na yunkurin kisan kai

- Rundunar 'yan Sanda ta yi zargin cewa Melaye da tawagar 'yan ta'addansa sun harbi wani Sajen Dajuma Saliu a jihar Kogi, a ranar 19 ga watan Yulin 2018

- Rundunar ta ce jami'anta zasu ci gaba da zaman jira a gaban gidan dan majalisar dattijan, har sai sun tabbata sun cafke Melaye

Rundunar 'yan sanda ta ce akwai wasu tambayoyi da take son Sanata Dino Melaye ya amsa a gabanta kan zargin da take masa na yunkurin kisan kai

Rundunar 'yan Sanda ta yi zargin cewa Melaye da tawagar 'yan ta'addansa sun harbi wani Sajen Dajuma Saliu tare da raunata shi, wanda ke kan aikinsa akan titin Aiyetoro Gbede zuwa Mopa a jihar Kogi, a ranar 19 ga watan Yulin 2018.

Kakakin rundunar, DSP Moshood Jimoh, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, biyo bayan wata mamaya da jami'an rundunar suka kai gidan Melaye da ke birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a.

KARANTA WANNAN: Badakalar WAEC: Dalilin da yasa bamu cafke hadimin Buhari ba - Rundunar 'yan sanda

Da duminsa: Rundunar 'yan sanda ta fara farautar Dino Melaye akan yunkurin kisan kai

Da duminsa: Rundunar 'yan sanda ta fara farautar Dino Melaye akan yunkurin kisan kai
Source: UGC

A cewarsa, masu bincike na rundunar 'yan sanda sun aikewa majalisar dattijai wasika, inda suka bukaci Melaye ya gurfana a ofishin rundunar na jihar Kogi, Lokoja, don amsa wasu tambayoyi kan zarginsa da ake yi, wanda kuma yaki amsa wannan gayyatar.

Jimoh ya ce: "Melaye da tawagar 'yan ta'addansa ne suka aikata laifin a jihar Kogi a ranar 19 ga watan Yulin 2018, inda suka harbi Saliu da ji masa ciwo. Har yanzu jami'in na kwance yana jinyar wannan rauni da ya samu daga harin sanatan."

Rundunar ta ce jami'anta zasu ci gaba da zaman jira a gaban gidan dan majalisar dattijan, har sai sun tabbata sun cafke Melaye.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel