Yan Majalisar da suka ci wa Buhari mutunci sakarkarun ’yan siyasa ne – Kungiyar MURIC

Yan Majalisar da suka ci wa Buhari mutunci sakarkarun ’yan siyasa ne – Kungiyar MURIC

- Kungiyar MURIC, ta nuna fushi akan ihun da ‘yan majalisar da suka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da ya ke gabatar da kasafin kudi

- Shugaban Kungiyar, ya ce dabi’ar ‘yan siyasar ya nuna tsantsar yaranta, jagaliyanci da kuma kidahumanci

- Ya kara da cewa abin da ya faru a lokacin da Buhari ke gabatar da jawabin sa, ya zama shaidar kukan da jama’a ke yi a baya cewa wannan majalisa da ke kan mulki yanzu, cike ta ke makil da ‘yan barababiya

Kungiyar Kare Hakkin Musulmi da ake kira MURIC, ta bayyana ‘yan majalisar da suka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari ihu a lokacin da ya ke gabatar da kasafin kudi, a matsayin shashashu, sakarkaru kuma dolayen ‘yan siyasa.

Wannan kakkausan furuci da MURIC ta yi, na kunshe ne a cikin wata doguwar takardar jawabi da ta aikawa manema labarai, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Shugaban Kungiyar, farfesa Ishaq Akintola, ya ce dabi’ar ‘yan siyasar ya nuna tsantsar yaranta, jagaliyanci da kuma kidahumanci.

Yan Majalisar da suka ci wa Buhari mutunci sakarkarun ’yan siyasa ne – Kungiyar MURIC

Yan Majalisar da suka ci wa Buhari mutunci sakarkarun ’yan siyasa ne – Kungiyar MURIC
Source: UGC

Akintola ya ce abin da ‘yan majalisar suka yi wa Buhari, ya nuna akwai yaranta da rashin sanin ya kamata a tattare su, sannan kuma ya nuna yadda suka zubar da kimar majalisar.

KU KARANTA KUMA: Kisan mutane uku: Dan majalisar wakilai daga Kano ya shiga tsaka mai wuya

Ya kara da cewa abin da ya faru a lokacin da Buhari ke gabatar da jawabin sa, ya zama shaidar kukan da jama’a ke yi a baya cewa wannan majalisa da ke kan mulki yanzu, cike ta ke makil da ‘yan barababiya, ‘yan ragabza, ‘yan bulkara da harmagaza, wadanda ba su san alkiblar da ta dace su bi ba.

MURIC ta kuma nuna bacin rai yadda sowar da aka rika yi har ta sa Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara bai samu damar karatan jawabin rufe taron ba. Ya ce wannan abin takaici ne kwarai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel