Direban Alex Badeh yana nan da ransa kuma yana samun sauki - NAF

Direban Alex Badeh yana nan da ransa kuma yana samun sauki - NAF

- Hukumar sojin saman Najeriya NAF ta ce direban Alex Badeh yana nan da ransa bai mutu ba duk da cewa an harbe shi

- Hukumar ta NAF ta kuma ce tsohon babban hafson tsaron yana tare da masu gadinsa a matsayinsa na tsohon soja

- Har ila yau, hukumar ta NAF ta ce ana samun nasara a binciken da ake gudanarwa domin gano wanda suka kashe marigayin

Hukumar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta ce direban tsohon babban hafson tsaro na kasa, Cif Alex Badeh yana nan da ransa kuma yana samun sauki akasin yadda wasu rahotanni suke cewa an kashe direban yayin harin da wasu 'yan bindiga suka kaiwa marigayin a ranar 18 ga watan Disambar 2018.

Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin jami'in hulda da jama'a na NAF, Air Commodore Ibikunle Daramola.

Direban Alex Badeh na nan da ransa duk da ya sha dalma
Direban Alex Badeh na nan da ransa duk da ya sha dalma
Asali: Twitter

Kazalika, Daramola ya ce NAF ta bawa marigayi Badeh masu gadinsa a matsayinsa na Janar mai anini hudu kuma tsohon babban hafson tsaro na kasa.

DUBA WANNAN: Badeh ya gana da Aisha da babban hadimin Buhari kafin a kashe shi - Rahoto

Ya ce, "Wasu rahotanni sunyi kuskure inda suka ce an kashe direban Badeh duk da cewa shima an harbe shi. Wasu kafafen yada labaran kuma sunyi ikirarin cewa ba a bawa tsohon shugaban tsaron masu gadi ba.

"NAF tana son fayyacewa karara cewa wannan ba gaskiya bane. da farko direban Badeh yana nan da ransa kuma yana samun sauki a wani asibitin NAF.

"Na biyu kuma, NAF ta bawa marigayi Badeh masu gadinsa a matsayinsa na Janar mai anini hudu kuma tsohon babban hafson tsaro na Najeriya."

Mai magana da yawun NAF ya kuma ce shugaban hafsoshin sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar ya ce NAF tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin gano wadanda suka kashe tsohon shugaban hafsoshin tsaron tare da tabbatar da ganin sun fuskanci hukunci.

Ya kara da cewa ana samun nasara a cikin binciken kuma a nan gaba hukumar za ta sanar da al'umma abinda ake ciki a lokacin da ya dace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel