Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Marigayi Alex Badeh

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Marigayi Alex Badeh

Wasu 'yan bindiga dadi da ba'a san ko suwaye ba sun harbe tsohon hafsan hafsoshin dakarun sojojin Najeriya Air Vice Marshal Alex Badeh har lahira akan hanyar sa ta dawowar daga gonar sa akan Abuja zuwa Keffi da daren yau.

Sanarwar da kakakin rundunar Ibukunle Daramola ya fitar ranar Talata da daddare ta ce 'yan bindigar sun kai hari kan motar da Mr Badeh ke ciki lokacin da yake kan hanyar komawa gida daga gonarsa a kan titin Abuja-Keffi.

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Marigayi Alex Badeh

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Marigayi Alex Badeh
Source: Facebook

KU KARANTA: Yadda 'yan bindiga suka kashe Marigayi Alex Badeh

A cewar sojin, tsohon babban hafsan tsaron na Najeriya ya mutu ne sakamakon raunukan da ya ji daga harbin bindigar da aka yi masa.

Ga dai wasu daga cikin abubuwan da ya kamata mu sani game da marigayin:

1. Alex Badeh ya rike mukamai da dama na soji, ciki har da babban hafsan sojin sama da babban hafsan tsaron Najeriya.

2. Mayakan kungiyar Boko Haram sun taba kai hari a kauyensu, ViMtim da ke jihar Adamawa inda suka kona gidansa sannan suka kashe wani dan uwansa a shekarun baya.

3. Sauka yayi daga mukamin sa na babban hafsan tsaron Najeriya.

4. Yana fuskantar tuhuma daga hukumar EFCC inda ake zargin sa da laifin satar kudi mallakin rundunar sojin sama ta kasar kimanin N3.9 bn, a lokacin da yake babban hafsan sojin kasar, domin sayen filaye.

5. An haifi tsohon babban hafsan tsaron na Najeriya a shekarar 1957 kuma ya soma aikin soja a 1977.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel