Manyan badakalar siyasa 5 da suka yi fice a 2018

Manyan badakalar siyasa 5 da suka yi fice a 2018

Kasancewar shekarar nan na bin wacce za’a yi zaben kasa, 2018 ta kasance shekara mai cike da al’amuran siyasa. Yan siyasa sun yi ta faman sauye-sauyen sheka, jam’iyyun siyasa na ta chanja manufofins, sannan sabbin yunkurin siyasa na ta billowa.

Bayan haka a shekarar an samu wasu manyan badakaloli na siyasa wanda har yanzu ana kan tunawa da su.

1. Kemi Adeosun

Manyan badakalar siyasa 5 da suka yi fice a 2018

Manyan badakalar siyasa 5 da suka yi fice a 2018
Source: Depositphotos

An zargi tsohuwar Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun da laifin amfani da jabun takardar shaida na NYSC ban da kuma laifin da tayi na kin yi wa kasa hidima.

Ana hakan sai wani tsohon Jami’in Hukumar bauta na kasa watau NYSC ya tabbatar da cewa satifiket din bogi ne a hannun Ministar.

2. Adebayo Shittu kan rashin yin bautar kasa

Manyan badakalar siyasa 5 da suka yi fice a 2018

Manyan badakalar siyasa 5 da suka yi fice a 2018
Source: UGC

A watan Satumba 2018, an samu ministan sadarwa, Adebayo Shittu da rashin yin bautar kasa wanda ya zama dole ga matasan da suka kammala kartunsu na jami’a.

Shittu yaki yin bautar kasa duk da cewan ya kammala jami’ar Ife yana da shekaru 25 a duniya.

Hakan yasa jam’iyyarsa ta APC hana masa yin takarar kujerar gwamnan jihar Oyo, bayan ta ki tantance shi.

KU KARANTA KUMA: Kasafin kudi: Yan majalisar wakilai sun yi ganawar sirri, sun kora jami’an tsaro da yan jarida

3. Sanata Ademola Adeleke

Manyan badakalar siyasa 5 da suka yi fice a 2018

Manyan badakalar siyasa 5 da suka yi fice a 2018
Source: Depositphotos

A watan Satumban 2018 ne dai rundunar 'yan sanda ta gurfanar da dan takarar gwamnan jihar Osun karkashin jam'iyyar PDP, Ademola Adeleke gaban kotu, kan zarginsa da satar jarabawar WAEC. Rundunar 'yan sanda na zargin Adeleke da hada baki da ma'aikatan makarantar Ojo-Aro community grammar, wajen samun sakamakon jarabawar na bogi, kuma hakan ne ma yasa rundunar 'yan sandata gurfanar a Adeleke tare da shugaban makarantar da wasu ma'aikata uku da ake zarginsu da aikata laifin tare.

4. Gwamna Abdullahi Ganduje

Manyan badakalar siyasa 5 da suka yi fice a 2018

Manyan badakalar siyasa 5 da suka yi fice a 2018
Source: Depositphotos

An zargi Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano da karbar rashawa bayan wata Jarida ta fito da bidiyoyin da ke nuna Gwamnan yana karbar Dalolin kudi daga hannun wadanda ake tunani ‘Yan kwangila ne a Jihar Kano.

Gwamna Ganduje dai ya musanya gaskiyar bidiyoyin da Jaridar Daily Nigerian ta saki inda yace siddabaru ne kurum na fasahar zamani. Haka kuma Kotu ta haramtawa ‘Yan Majalisar dokokin Jihar gabatar da wani bincike a kan lamarin.

5. Timothy Owoeye

Manyan badakalar siyasa 5 da suka yi fice a 2018

Manyan badakalar siyasa 5 da suka yi fice a 2018
Source: UGC

A watan Satumba ne aka ga wani shahararren bidiyo da ke nuna Timothy Owoeye, dan majalisa a majalisar dokokin jihar Osubn, inda wasu maza k eta dukansa bayan sun kama shi yana wankan magani cikin tsakar dare a kasuwa.

An dai zargi dan majalisan wanda a yanzu shine shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar da aikata hakan saboda wani manufa nashi na siyasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel