Yanzu-yanzu: Sanata Ahmed Aruwa ya mutu

Yanzu-yanzu: Sanata Ahmed Aruwa ya mutu

Labarin da ke shigo mana yanzu-yanzu daga jihar Kaduna na nuna cewa Allah ya yiwa babban dan siyasa kuma tsohon sanatan Kaduna, Ahmed Aruwa, ya rasu.

Majiya daga iyalanshi sun bayyana cewa ya rasu ne da safiyar yau Asabar kuma za'ayi janaizarsa a masallacin Sultan Bello misalin karfe 1.

Aruwa ya kasance Walin Hadejia, ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 1999 da 2007.

A majalisar, ya rike kujeran shugaban kwamitin sufurin jirgin sama, ayyuka da gidajem harkokin yan sanda, aikin noma da kuma kasafin kudi.

Ya bar mata daya da yara 4.

Muktar Ahmad Aruwa ya taso ne daga babban gida, sannan kuma ya shiga siyasa inda ya fara shiga Majalisar Dattawa a karkashin Jam’iyyar adawa ta ANPP a Jihar Kaduna. Aruwa ya nemi Gwamna amma bai yi nasara ba.

Legit Hausa ta tsakuro maku kadan daga cikin tarihin wannan Bawan Allah:

1. Sanata a 1999

Mukhtar Aruwa ya wakilici Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa a karkashin Jam’iyyar adawa ta APP bayan dawowa mulkin farar hula a 1999. Aruwa yayi tashe a Majalisa kan batun shari’ar Musulunci da yunkurin saida kadarorin Gwamnati.

2. Tazarce a Majalisa

Sanata Aruwa ya sake samun nasarar komawa kujerar sa a 2003 inda ya cigaba da fafatuka a Majalisar Dattawa. Mukhtar Aruwa yana cikin wadanda su ka rika ba Shugaban kasa Oluesgun Obasanjo ciwon kai a Majalisar Tarayya a wancan lokaci.

3. Takarar Gwamna

Mukhtar Aruwa ya nemi Gwamnan Jihar Kaduna a 2007 inda har ya lashe zaben fitar da gwani a karkashin Jam’iyyar ANPP. Sai dai Jam’iyyar ta hana sa takara, ta tsaida Sani Sha’aban saboda wasu dalilai inda ya daura laifin kan Jagoran ANPP, Muhammadu Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel