wani mutumi ya ci mahaifar matar sa
Wani mutumi mai shekaru 32 a duniya wanda aka kira da suna Ross Watson, yana ta yawo a kafofin watsa labarai saboda wasu hotuna da dama da bidiyon sa da ya watsa a lokacin da yake cin mahaifar matarsa a matsayin abincin safe sati daya bayan an haifa masa da namiji.
Watson bai ci mahaifar tata haka kawai ba sai da ya gauraye si da barkono da kayan miya, ya bayyana cewa ‘yana da kyau da gina jiki’. A cikin bidiyon, ya zauna a teburin cin abinci tare da danyen mahaifa a faranti, wani faranti dauke da dafafiyar mahaifa da kuma wani dauke da abincin turawa da farantin wake, da gas ashen biredi.
KU KARANTA KUMA: Yanda aka zargi ministan harkokin Niger Delta da aikata zamba
“Ina yawan cewa zan ci mahaifar mata ta. Babu shakka ya fi kyau idan aka dafa. Mintina tara a yayin dafa wa da kuma kimanin mintina 10 a yayin ci. Cheers” ya ce yayin da ya fara cin Karin sa.
Ta yaya mutumin dake cikin hankalinsa zai ci abu irin haka, ina matar tasa take a lokacin da yake cin mahaifar?
A jiya ne muka samu rahotanni kan mutumin da yayi yunkurin yin batanci da al'Qur'ani mai girma ta hanyar zana rubutun cross a tsakiyar littafin Allah. inda Ubangiji ya nuna masa mu'ujizar sa domin hannun nasa ya makale a jiki, kuma duk wani kokari da akayi don aka an cire hannun daga jikin Qur'anin ya gagara.
Asali: Legit.ng