An damke matashi da laifin kisan mahaifinsa a Abuja

An damke matashi da laifin kisan mahaifinsa a Abuja

Hukumar yan sandan Najeriya ta damke wani matashi dan shekara 22 da laifin kisan mahaifinsa. Marigayin mai suna, Alhaji Hussaini Usman, wanda babban dan kasuwa ne kuma dan kwangila ya rasu ne ranan 28 ga watan Oktoba a gidansa dake Abdulkareem Adisa Estate, Apo.

Masu bincike sun kwashe wata daya suna bincike kuma sunyi ittifakin cewa haifaffen cikin mamacin, Huzaifa Hussaini Usman, ne wanda ake zargi da kisan.

Majiya masu ilimi kan al’amarin sun bayyana cewa wannan labara ya fara yaduwa ne a ranan cewa yan fashi sun kai hari gidan kuma sun kasha dattijon.

“Ance yana hanyar zuwa masallaci ne misalign karfe 5 na safe tare da Huzaifa yayinda yan fashin suka kawo masu hari,” Wani na kusa da gidan.

Makwabta sun yi kokarin kira Alhajin yayinda sukaji hayaniya na fitowa daga gidansa amma bai dauki waya ba. Sai suka garzaya gidan.

An damke matashi da laifin kisan mahaifinsa a Abuja

An damke matashi da laifin kisan mahaifinsa a Abuja
Source: Facebook

KU KARANTA: Ba mu bukatan Okorocha da Amosun - Oshiomole

Majiyar ya cigaba da cewa: “Yayinda suka shiga, sun ga gawar Alhaji a kasa. Wadanda suka shiga suka cewa akwai lauje cikin nadi saboda sun dade suna kwankwasa kofa kafin aka bude musu.”

Huzaifa ya fadawa mutane cewa kafin ya farga, yan fashin sun kasha mahaifin kuma sun tafi. Sai ya ja gawan mahaifin zuwa daki sannan ya kira mahaifiyarsa kafin aka sanar a Masallaci.”

Jama’an unguwa sunce karya ne babu wanda ya kira mutanen masallaci. Jama’an ne suka zo gidan da kansu.

Bugu da kari, an ga alamun kakkarcewa a jikinsa sai aka tambayensa ta yaya ya kakkarce tun ya ce yan fashin basu tabashi ba.

Wannan zargi ya kara girma ne yayinda aka lura Huzaifa ya ki halartan jana’izan mahaifinsa suk da cewa shi kadai ne namiji a gidan a lokacin.

Da aka bukaci bincike kan gawar, iyalan mamacin suka kiya. Sun ce kawai a birneshi bisa ga koyarwan addinin Musulunci.

Majiya na kusa da huku yace makonni biyu aka gayyaci Huzaifa ofishin yan sanda inda ya bayyana cewa da gaske ya baiwa wasu kudi su kasha wani Isma’il amma ba mahaifinsa ba.

Kakakin hukumar yan sandan Abuja, DSP Anjuguri Manzah, ya tabbatar da wannan labara kuma an shigar da shi kotu.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel