Da dumi dumi: Wanda ya kafa kungiyar Yarabawa ta OPC, Frederick Fasehun ya mutu

Da dumi dumi: Wanda ya kafa kungiyar Yarabawa ta OPC, Frederick Fasehun ya mutu

Wanda ya kafa kungiyar Yarabawa ta Oodua Peoples Congress (OPC), Dr Frederick Fasehun ya mutu. Ya mutu ne da misalin karfe 1:00 na safiyar ranar Asabar a sashen kula da marasa lafiya na musamman da ke cikin asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas da ke Ikeja (LASUTH).

Babban mashawarci kan harkokin watsa labarai ga Fasehun, Mr Adeoye Jolaosho, ya sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, a Legas, a ranar Asabar.

Ya ce jagoran kungiyar ta OPC ya mutu ne da misalin karfe 1:00 na safiyar ranar Asabar a sashen kula da marasa lafiya na musamman da ke cikin asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas da ke Ikeja (LASUTH).

KARANTA WANNAN: Sakamakon jibgar jami'in VIO: Kotu ta garkame wani direban babbar mota

Da dumi dumi: Wanda ya kafa kungiyar Yarabawa ta OPC, Frederick Fasehun ya mutu

Da dumi dumi: Wanda ya kafa kungiyar Yarabawa ta OPC, Frederick Fasehun ya mutu
Source: Facebook

"A ranar Laraba, Baba ya fara rashin lafiya, inda aka garzayawa da shi sashen kula da marasa lafiya na musamman da ke cikin LASUTH.

"Ya mutu ne a safiyar yau. Hankulanmu gaba daya a tashe yake, mun girgiza matuka," a cewarsa.

NAN ta ruwaito cewa marigayi Fasehun na daga cikin jiga jigan kungiyar gamayayyar demokaradiyya ta kasa (NADECO)

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel