Iyaye, dalibai, masu ruwa da tsaki sun fara kokawa kan dadewar yajin aikn ASUU

Iyaye, dalibai, masu ruwa da tsaki sun fara kokawa kan dadewar yajin aikn ASUU

- Iyaye, dalibai da kuma masu ruwa da tsaki afannin ilimi, sun bayyana cewa yajin aikin da ASUU ta shiga, na iya jefa wasu dalibai aikata ta'addanci da sauran munanan dabi'u

- Shugaban kungiyar NANS, ya ce al'adar shiga yajin aiki da ake yi a kasar kowacce shekara, shine ke samar da dalibai marasa ilimin abubuwan da ya kamata ace ana koyar da su

- Perpetual Ahanonye, ta koka kan yadda yajin aikin yaki ci-yaki cinyewa a fannin ilimi, wanda hakan ya tilastata komawa ga sana'ar hannu kafin zuwan ranar janye yajin aikin

Iyaye, dalibai da kuma masu ruwa da tsaki afannin ilimi, sun bayyana damuwarsu kan yadda yajin aikin da ASUU ta shiga, yaki ci-yaki cinyewa, wanda da yawansu ke ganin cewa, dogon lokacin da ake ci gaba da dauka na iya jefa wasu dalibai aikata ta'addanci da sauran munanan dabi'u.

Shugaban kungiyar dalibai na ta kasa NANS, Danielson Akpan, a wata hira da akayi da shi kai tsaye ta kafar gidan rediyo, ya ce al'adar shiga yajin aiki da ake yi a kasar kowacce shekara, shine babban dalilin samar da dalibai da suka kammala karatu ba tare da ilimin abubuwan da ya kamata ace ana koyar da su ba.

KARANTA WANNAN: Babbar asara: Wata mota mai dauke da kayan N500m ta kone kurmus a Kebbi

Iyaye, dalibai, masu ruwa da tsaki sun fara kokawa kan dadewar yajin aikn ASUU
Iyaye, dalibai, masu ruwa da tsaki sun fara kokawa kan dadewar yajin aikn ASUU
Asali: Facebook

Ya yi ikirarin cewa mafi akasarin lokutan da ake komawa yajin aikin, akan tilasta dalibai fara jarabawa ba tare da kammala koyar da darussan zangon ba, yana mai jaddada muhimmancin cusa dalibai, wadanda sune ainihin masu ruwa da tsaki, a harkokin da suka shafi yanke hukunci da sasanci a duk lokacin da kungiyar ASUU ke shirin shiga yajin aiki.

Wata daliba jami'ar jihar Imo, wacce ya ke aji ukku, Perpetual Ahanonye, ta koka kan yadda yajin aikin yaki ci-yaki cinyewa a fannin ilimi, wanda hakan ya tilastata komawa ga sana'ar hannu kafin zuwan ranar janye yajin aikin.

Haka zalika, Mrs. Joy Okoro, ta ce gwamnati taki duba bukatun malaman jami'ar saboda 'yanyansu na can suna karatu a kasashen turai, hakan ya sa yajin aikin ba zai wani dame su ba, kana ta roki kungiyar ASUU da ta duba illolin da yajin aikin ya janyo, don janyewa.

Kawo karshen yajin aikin, kamar yadda suka fada, ya zama wajibi duba da irin tarin illolin da ya ke da shi ga dalibai da kuma al'ummar baki daya, musamman ganin cewa babban zabe na 2019 na gabatowa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng