Badakalar biliyan N5.7bn: Tsohon hadimin Shema ya kwance ma sa zani a gaban kotu
Nasiru Ingawa, tsohon mai bawa tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema, shawara a kan kudaden tallafin man fetur na bayar da shaida a gaban kotu a yau, Talata.
Bayan ya yi rantsuwa a gaban alkali, Ingawa ya bayyana yadda tsohon gwamna Shema ya umarce shi da ya kashe kudaden tallafin man fetur, biliyan N5.7bn, da gwamnatin tarayya ta bawa jihar Katsina.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar an gurfanar da Shema ne bisa tuhumar sa da aikata laifuka 26 da su ka hada da almundahana da karkatar da kudaden jama'ar jihar Katsina.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ce ta gurfanar da tsohon gwamnan tare da neman kotu ta hukunta shi kamar yadda sashe na 15(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Ingawa ya sanar da kotu cewar shine mai bawa Shema shawara a kan kudaden SURE-P daga watan Yuni na shekarar 2014 zuwa watan Mayu na shekarar 2015.
"Na tuna sarai cewar gwamna Shema ya fada min cewar za mu yi amfani da kudin ne domin yakin neman zabe.
"Ya umarce ni nayi amfani da rabin kudin duk shirye-shiryen da aka gabatar a rubuce za a yi, sannan na ajiye ragowar domin amfani da su wajen yakin neman zabe," a cewar Ingawa.
DUBA WANNAN: Machina: Gari a arewa da macizai ke kaiwa Sarki gaisuwa
Sannan ya kara da cewar akwai lokutan da zai gabatar da wani aiki a rubuce, gwamnan zai umarce shi ya fitar da kudin amma ba za a yi amfani da su domin yin aikin ba.
Kazalika ya bayyana cewar wasu lokutan gwamnan kan bukace shi ya kawo ma sa kudi ko kuma ya umarce shi ya bawa wani kudi daga cikin kudin na SURE-P.
"Muna fitar da madarar kudi ne daga asusun mu SURE-P, mu na bayar da cakin fitar da kudi idan an yi wasu aiyuka," Ingawa ya sanar da kotun.
Bayan kammala suraren Ingawa ne sai mai shari'a, Jastis Hadiza Rabiu Shagari, ta daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Janairu na shekarar 2019.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng